Cece-kuce ya tsananta bayan budurwa ta gwangwaje saurayinta da Keke Napep, ta bar ɗan uwanta yana fama ba aiki

Cece-kuce ya tsananta bayan budurwa ta gwangwaje saurayinta da Keke Napep, ta bar ɗan uwanta yana fama ba aiki

  • Wani matashi ya yi wata wallafa a Facebook inda ya ke bayyana yadda wata budurwa ta gwangwaje saurayin da zata aura da Keke Napep amma ta bar dan’uwanta yana fama
  • Matashin ya bayyana farincikinsa akan yadda Ubangiji ya azurta shi da ‘yar uwa mai kaunarsa wacce ta tallafa wa rayuwarsa kwarai
  • Budurwar kuma a bangarenta ta bayyana hujjojin ta akan zabar tallafa wa saurayinta a maimakon dan’uwanta wanda dalilan su ka ya janyo surutai

Wani dan Najeriya, Uzoukwu Anayo ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta inda ya ke alfahari da yadda Ubangiji ya azurta shi da ‘yar uwa mai jajircewa, inda yace da babu ita da bai kai inda yake ba a rayuwa.

A wallafar da ya yi a Facebook, Anayo ya yi amfani da damar wurin shawartar mata masu tallafa wa samarin da zasu aura maimakon ‘yan uwansu na jini.

Cece-kuce ya tsananta bayan budurwa ta gwangwaje saurayinta da Keke Napep, ta bar ɗan uwanta yana fama ba aiki
Cece-kuce y barke bayan wata ta siya wa saurayi Keke Napep, ta bar dan uwanta na fama ba aiki. Hoto: Uzoukwu Anayo, Keke Napep
Asali: Facebook

Anayo ya kafa hujja ta hanyar bayar da labari akan wata mata wacce ta bar dan’uwanta amma ta tallafa wa saurayin da su ka yi alkawarin aure da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana yadda wata budurwa ta bar dan’uwanta yana yawo a gari babu aiki amma ta siya wa wanda zata aura Keke Napep.

Budurwar ta bayyana dalilanta na qyale dan’uwanta

A cewarsa a lokacin da ya tambayeta dalilinta na share dan’uwanta tace masa ne idan ya yi aure wata macen daban ce zata mori guminsa.

Yayin da ya yi mamaki akan amsarta, Anayo ya ce wannan dalilin ba kwakkwara bane da har zai sa ta bar dan’uwanta yana fama da talauci.

Kamar yadda ya wallafa:

“Wata budurwa ta siya wa saurayin da zata aura Keke Napep yayin da ta bar dan’uwanta a titi yana yawo babu aiki babu sana’a.

“Ban yarda da dalilin da ta bani na yin hakan ba; cewa ta yi idan ta taimaki dan’uwanta yanzu zai koma ya yi aure wata matar ta mori guminta. Kalli wata hujja fah? Akan wannan banzan dalilin ne zata iya barin dan’uwanta yana fama.”

Martanin 'yan Najeriya

King Dave ya ce:

“Tabbas dan’uwa.. Ya kamata wasu matan su sauya tunaninsu akan aure. Su san abinda ya kamata.. Wasu matan idan sun kosa suyi aure haka suke yi.. Idan zan ba mata shawara anan, ki tallafa wa mijin ki bayan kunyi aure ne ba kafin ya aure ki ba.. Don zuciyarki zata iya fashewa idan ya kulla miki wani abin.”

Promise Loveth ta ce:

“Yar uwa, dan uwana zan fara kulawa... Saboda duk daren dadewa dan’uwanka naka ne.”

Rukayat Abike Mahmud tace:

“Ka gama magana dan’uwa.”

Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi

A wani labarin, matar da ta yi karar likitan mahaifiyarta a kotu saboda ta bari an haife ta za ta samu miliyoyi a matsayin diyya, Times Now ta ruwaito.

Evie Tombes ta yi karar likitan mahaifiyarta ne kan 'kuskure yayin daukan ciki' don an haife ta da wani cuta da ake kira spina bifida a 2001. Cutar da ba a cika samunsa ba yana shafar kashin baya ne kuma wasu lokutan yana nakasar da mutum har abada.

Hakan yasa Evie a duk rayuwarta sai an jona mata robobi na magani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel