Bayan Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya wasu ka'idoji kan NETFLIX da sauransu

Bayan Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya wasu ka'idoji kan NETFLIX da sauransu

  • Gwamnatin shugaban kasa Buhari ta shirya tsara yadda ake amfani da kafafen yada bidiyo kai tsaye a kasar nan
  • Gwamnati ta bayyana damuwarta, inda ta ce watakila a yi amfani da kafafen wajen bata damar dimokradiyya
  • Gwamnatin ta bayyana yadda ta tsara tafiyar da wannan batu, inda tace hakan zai taimaka sosai ga ci gaban kasa

Legas - Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirye-shiryen ta na fitar da tsarin amfani da kafafen yada bidyo irinsu NetFlix, kamar yadda ta yi ikirarin cewa za a iya amfani da su don "haifar da hargitsi" da kuma lalata tsarin dimokradiyyar Najeriya.

A wani taro na kwanaki biyu, gwamnatin Buhari da masu ruwa da tsaki a masana'antun kirkira sun tattauna yiyuwar duba ayyukan kafafen yada bidiyo kai tsaye tare da tacewa da kayyade amfani dasu.

Kara karanta wannan

Auren jarumar Kannywood Maryam Waziri: Ango da amarya sun saki zafafan bidiyon bikinsu

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed
Bayan Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya wasu ka'idoji kan NETFLIX da sauransu | punchng.com
Asali: Facebook

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa shahara da kuma bukatuwa ga shirye-shiryen kai tsaye a Najeriya ya karu saboda Korona don haka za a sa ka’idoji.

A baya dama Lai Mohammed ya ce gwamnati za ta duba yiwuwar fitar da tsari kan duk wasu kafafen yada labarai, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Ministan wanda Daraktar Watsa Labarai da Fasaha, Comfort Ajiboye, ta wakilta, ya sake nanata ra’ayinsa na tsawon shekaru cewa za a iya amfani da kafafen sada zumunta da yada labarai “don haifar da hargitsi da lalata tsarin dimokradiyya.”

Hukumar tace fina-finai da bidiyo ta kasa (NFVCB) ce ta shirya taron a ranar Laraba a Legas, tare da kwararru da masu ruwa da tsaki a harkar nishadi da kirkira.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

A jawabinsa na bude taron, Babban Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar NFVCB, Adedayo Thomas, ya ce taron an shirya shi ne don samar da tsare-tsare na daidaita hanyoyin yada labarai da samar da bayanai a Najeriya.

Thomas ya ce:

"Tare da sama da 50% cikin 100% na hulda da yanar gizo, ya zama wajibi a kira wannan taro don tattaro masu ruwa da tsaki da 'yan majalisa a cikin tattaunawa ta yadda za a samar da tsare-tsare masu inganci kan ka'idojin masu yada bidiyo da masu samar da bayanai."

Shugaban hukumar ta NFVCB ya ce kafofin yada bidiyo kai tsaye ba sa iya sarrafa kansu, dalilin da ya sa a yanzu ake tattauna ayyukansu a wurin taron da taken, “Nigeria Digital Content Regulation”.

Thomas, duk da haka, yayi alkawarin cewa:

"Makasudin sanya ka'idar ba za a yi shi don hana kirkira bane sai dai don haifar da tsari da karfafa gasa mai kyau don ci gaban tattalin arziki da zamantakewa."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake mutuwa daga cutar Maleriya

A wurin taron, akwai Daraktan manufofin jama'a na kafar Netflix, yankin kudu da hamadar sahara, Shola Sanni, Sahara Reporters ta ruwaito.

Mahalarta taron sun hada da mambobin kungiyoyin daban-daban na Nollywood da suka hada da Actors Guild of Nigeria (AGN) da Directors Guild of Nigeria (DGN).

Sauran sun hada da Association of Producers (AMP), Theater and Movie Practitioners Association of Nigeria (TAMPAN), da dai sauransu.

Har ila yau, akwai wakilan kafafen yada bidiyo na kasashen waje, Free To Air (FTA), masu kula da Pay Tv da sauran masu kirkirar bidiyo.

Buhari zai gyara Najeriya tsaf kafin ya sauka a mulki a zaben 2023, inji Sanata

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya, Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara gyara kasar nan kuma zai bar mulki a 2023 a matsayin jarumin kasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Amosun ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake kwatanta yadda jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta shafe shekaru shida tana mulki da kuma yadda jam’iyyar PDP ta yi mulki na shekaru goma sha shida a kasar.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Amsoun, kwararren akanta ya bayyana hakan a yayin wani taron tunawa na bikin mako na shekara ta 2021 na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a jihar Oyo a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel