Majalisa ta gayyaci shugaban INEC kan batun kudade N500bn na zaben fidda gwani

Majalisa ta gayyaci shugaban INEC kan batun kudade N500bn na zaben fidda gwani

  • Ana rade-radin cewa, kasasfin kudin zaben fidda gwanin kai tsaye gabanin babban zabe zai ci biliyoyin kudi a Najeriya
  • Wannan yasa majalisar wakilai ta Najeriya ta gayyaci shugaban hukumar INEC domin ya bayyana gaskiya
  • Majalisar ta ce yanzu lokacin da ya dace yayi bayani ne saboda a halin yanzu kasafin kudin kasar na hannun majalisar dokokin kasar

Abuja - Majalisar Wakilai ta gayyaci Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, domin ya bayyana irin kudaden da ake kashewa wajen gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan da dan majalisa mai wakiltar mazabar Yagba East/Yagba West/Mopa-Muro na jihar Kogi, Rep. Leke Abejide ya gabatar da kudirin gaggawa ga jama'a a ranar Alhamis a Abuja yayin zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda gidajen marayu za su cike fom din tallafin marayu na mawaki Davido

Majalisar wakilai ta Najeriya
Da dumi-dumi: Majalisa ta gayyaci shugaban INEC kan kudin da za a kashe a zaben fidda gwani | channelstv.com
Asali: Facebook

Yakubu zai gurfana a gaban kwamitocin kasafin kudi da harkokin zabe domin yin magana a kan lamarin, Punch ta ruwaito.

A cikin kudirin, Abejide ya ja hankali kan rade-radin da ake yi cewa za a kashe sama da Naira biliyan 500 ga jam’iyyun siyasa domin gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye gabanin babban zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce kudin da za a kashe zai iya kawo cece-kuce kan makomar dokar zabe ta 2021 da har yanzu take gaban shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

Kudirin ya dauki zaben fidda gwani kai tsaye a matsayin tsarin zaben 'yan takarar jam'iyyun siyasa don zaben gaba.

Ya yi nuni da cewa INEC ce ta fi dacewa ta fadi komai kan kudin da za a kashe a zaben fidda gwanin kai tsaye tunda ita ce alkaliyar da ke kula da zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa da na manyan zabuka.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Buhari ya cancanci jinjina kan yadda ya shawo kan matsalar tsaro

A cewarsa:

“Wasu mutane sun ce zai ci N500bn. Wannan hasashe ne kawai domin kudin zaben fidda gwani na iya kasancewa cikin kasafin kudin INEC.”

Ya bayyana cewa lokaci mafi dacewa na gayyatar Yakubu shine yanzu da kasafin kudin 2022 yake gaban majalisar dokokin kasar.

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wa majalisar wajen yanke shawara kan kasafin kudin da ya dace.

Shawarin kakakin majalisa

Da yake ba da shawarinsa bayan an zartar da kudirin, Kakakin Majalisar Gbajabiamila ya ce:

"Kwamitocin hukumar INEC da kasafin kudi, da fatan za a gayyaci shugaban INEC domin ya ba mu abin da za a iya kashewa a zaben fidda gwanin kai tsaye."

Idan baku manta ba, INEC ta ce tana da duk wata dama ta yin zaben fidda gwanin kai tsaye ko ba kai tsaye ba, kamar yadda This Day ta ruwaito.

A wani labarin, Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce za ta bayyana matsayarta kan tsarin daidaita dokar zabe nan da sa’o’i 48, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan APC a Arewa sun fara gangamin nuna goyon baya ga Okorocha ya zama shugaba a 2023

Jam’iyyar PDP wadda tun da farko ta nuna rashin amincewa da shigar da zaben fidda gwani kai tsaye, ta ce kowace jam’iyyar siyasa tana da ‘yancin tantance yadda za ta zabi ‘yan takararta.

Jam’iyyar adawar a cikin wata sanarwa da kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar, ta ce babu wata jam’iyyar siyasa da ke da hurumin kakaba tsarin zaben fidda gwani a kan wata jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel