Dalla-dalla: Yadda gidajen marayu za su cike fom din tallafin marayu na mawaki Davido

Dalla-dalla: Yadda gidajen marayu za su cike fom din tallafin marayu na mawaki Davido

Kwanaki kadan da suka gabata, tauraron mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa Naira miliyan 200 da ya samu daga abokansa da masoyansa a shafukan sada zumunta bayan tambayarsu, zai bayar dasu ga gidajen marayu a fadin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa zai kara Naira miliyan 50 a kan kudin da za a ba wa gidajen marayun, inda zai zama Naira miliyan 250.

Bayan haka Davido ya bayyana wani kwamiti mai mutane biyar da zai kula da yadda za a raba kudaden ga gidajen marayun da suka cancanta.

Tallafin marayu na Davido
Dalla-dalla: Yadda gidajen marayu za su cike fom din tallafin marayu na mawaki Davido | Hoto: @davido
Asali: Instagram

A wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Instagram, tauraron mawakin ya bayyana cikakken bayani kan yadda gidajen marayu za su nemi wannan tallafin.

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

A cewarsa, gidajen marayun da gwamnati ta amince da su ne kadai suka cancanci wannan tallafin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An fara cike fom din neman tallafin kudaden daga ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba kuma za a rufe a ranar Alhamis 2 ga watan Disamba.

Yadda ake neman tallafin

1. Masu gudanar da gidajen marayun da suka cancanta su bi wannan tashar yanar gizon da ke kasa: https://linktr.ee/davidoorphanagedonations

2. Bayan bude tashar ta yanar gizo, a danna maballin 'orphanage registration link' don ci gaba zuwa mataki na gaba

3. Sakon maraba zai biyo baya, bayan haka sai ku danna inda aka rubuta 'continue' don karanta ka'idodin cike fom din

5. Bayan amincewa da ka'idodin da aka lissafa, zaku iya ci gaba da cike fom din sannan ku mika shi daga baya

Tambihi

  • Ana sa ran babban jami'i ko wanda ya kafa gidan marayun ne zai yi rajistar a madadin gidan marayun
  • An shawarci masu neman tallafin su cika kowane gurbi kuma dalla-dalla na fom din yadda ya dace
  • Ana kuma sa ran a hada takaddun da suka dace hade da fom din
  • Duk bayanan da aka shigar za a bi diddigi don tabbatarwa, rashin daidaito ko bayanan karya zasu haifar da rashin damar samun tallafin
  • Kwamitin bayar da kudaden na iya gudanar da binciken gani da ido ba tare da masu nema ba
  • Masu neman karin bayani za su iya aika sakon imel zuwa: davido.orphangedonations@gmail.com

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a ban daki

Atiku ya tura wa Davido sako bayan mika kudin da aka tara masa ga marayu

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana yabonsa ga mawaki David Adeleke (Davido) bisa tallafin da ya mika ga marayu a fadin Najeriya.

A makon da ya gabata ne Davido ya bayyana bukata ga abokai da masoyansa cewa, yana bukatar su tura masa kudade cikin asusun bankinsa domin shagalin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Jim kadan bayan da ya tara sama N200,000, Davido ya bayyana cewa, zai mika kudin ne ga cibiyoyin marayu a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel