Da Duminsa: MTN da wasu kamfanoni 2 sun cancanci fara amfani da 5G, inji NCC

Da Duminsa: MTN da wasu kamfanoni 2 sun cancanci fara amfani da 5G, inji NCC

  • Gwamnatin Najeriya ta amince wa kamfanonin sadarwa guda uku fara amfani da tsarin sadarwar 5G a kasar
  • Kamfanonin MTN, Airtel da Mafab ne suka samu nasarar lashe gwanjon da hukumar NCC ta shirya kan tsarin na 5G
  • A baya gwamnatin Najeriya ta amince a fara gwada sabis din 5G a Najeriya, inda tace ta tabbatar da bai da wata illa

Najeriya - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da wasu kamfanonin sadarwa guda uku da suka cancanta a matsayin wadanda aka amince da su a gwanjon 5G mai gudun 3.5GHz.

An yi gwanjon ne don tura fasahar amfani da tsarin sadarwa na 5G a cikin kasar nan daga Janairun 2022, The Nation ta ruwaito.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC)
Da dumi-dumi: Kamfanonin layukan waya 3 sun cancanci fara gwada tsarin 5G, NCC | businessday.ng
Asali: Twitter

Kamfanonin sun hada da MTN Nigeria plc, Mafab Communications Limited da kuma Airtel Networks Limited.

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta NCC, Dr Ikechukwu Adinde.

Nigerian Tribune ta ruwaito shi yana cewa:

“Dangane da ka’idojinta na gwanjon keke da keke, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da cewa kamfanonin sadarwa guda uku sun cancanta a matsayin wadanda aka amince da su na yin gwanjon tsarin 3.5 gigahertz (Ghz) mai zuwa don dasa tura hanyoyin sadarwa na 5G a kasar."

Gwamnatin Buhari ta amince a fara aiki da fasahar 5G a Nigeria

A baya, Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nigeria, FEC, ta amince a fara aiwatar da tsarin fasahar sadarwar ta 5G.

An amince da fara aiwatar da shirin shimfida fasahar ta 5G din a yayin taron mako-mako na FEC da Shugaba Muhamamdu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin El-Rufa'i za ta sallami Malamai 233 kan laifin amfani da takardun boge

Femi Adeluyi, hadimin ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim (Pantami) ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel