Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari Ta Amince a Fara Aiki Da Fasahar 5G a Nigeria

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari Ta Amince a Fara Aiki Da Fasahar 5G a Nigeria

  • Gwamnatin Nigeria ta amince da fara amfani da sabuwar fasahar sadarwa na 5G
  • Majalisar Zartarwa na Tarayya, FEC, ce ta bada amincewar a ranar Laraba 8 ga watan Satumban 2021
  • Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman taron na FEC a fadarsa da ke Abuja

FCT, Abuja - Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nigeria, FEC, ta amince a fara aiwatar da tsarin fasahar sadarwar ta 5G.

An amince da fara aiwatar da shirin shimfida fasahar ta 5G din a yayin taron mako-mako na FEC da Shugaba Muhamamdu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari Ta Amince a Fara Aiki Da Fasahar 5G a Nigeria
Shugaba Muhammadu Buhari da ministocinsa yayin taron FEC. Hoto: Femi Adeluyi
Asali: Facebook

Femi Adeluyi, hadimin ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim (Pantami) ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook.

Sanawar ta ce:

Kara karanta wannan

Mataimakin Dirakta a ma'aikatar gwamnati ya hallaka kansa ranar da EFCC ta gayyaceshi

"An shafe shekara biyu ana aiki kan tsarin aiwatar da fasahar ta 5G saboda tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma wayar da kan mutane game da sabuwar fasahar.
"An tuntubi masu ruwa da tsakin da ya dace. An kuma duba rahoton gwajin 5G din da aka yi na watanni uku da aka fara a ranar 25 ga watan Nuwamban 2019.
"An yi nazarin rahoton yadda ya kamata an kuma duba tasirin 5G kan lafiya da tsaro a Nigeria."
"Manyan hukumomin kasa da kasa kamar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da Kungiyar Sadarwar ta kasa da kasa, ITU, na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar cewa 5G bata da illa ga lafiya."

Sanarwar ta Femi Adeluyi ta cigaba da cewa Ma'aikatar Sadarwar Nigeria ta ce fasahar 5G na da amfani fiye da sauran fasahar sadarwa da ake amfani da su yanzu.

Wasu daga cikin amfanin sun hada da saurin isar da sakonni, inganta lafiyar batirin na'urorin sadarwar, samar da hotuna masu kyawu da sauransu.

Kara karanta wannan

Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

Kasashe da dama tuni sun fara amfani da fashar da 5G kuma suna morar amfaninsa.

Kasashen sun hada da Amurka, Burtaniya, Jamhuriyar Korea, Afirka ta Kudu da Lesotho.

Labari Mai Daɗi: Jihar Kogi Za Ta Fara Samar da Man Fetur, Yahaya Bello

A wani labarin daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa yanzu jihar Kogi ta na samar da man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da manema labaran cikin gidan gwamnati suka yi da shi bayan ya kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Gwamnan ya ce ya kai wa shugaban kasa ziyara ne don godiya bisa karamcin da ya yi masa da kuma yi wa mutanen sa sambarka, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel