Auren jarumar Kannywood Maryam Waziri: Ango da amarya sun saki zafafan bidiyon bikinsu

Auren jarumar Kannywood Maryam Waziri: Ango da amarya sun saki zafafan bidiyon bikinsu

  • Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Waziri ta auri tsohon tauraron Super Eagles, Tijjani Babangida
  • Jarumar fim din ta bayyana a kafafen sada zumunta inda ta yi albishir da batun aurenta bayan ta ce wani ya yi wuff da ita
  • Bidiyon bikin auren Maryam da Tijjani sun yi ta zagayawa a yanar gizo yayin da masoya ke taya su murna

Gombe - Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Waziri da tsohon dan wasan Super Eagles, Tijani Babangida, sun cika masoya, yayin da aka daura aurensu.

Shahararrun ma'auratan sun yi auren kwanan nan inda suka nuna dimbin masoyansu a shafukan sada zumunta yadda aka sha biki.

Rahotanni sun ce an daura aurensu ne a ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba a garin Kaltungo da ke jihar Gombe.

Auren Maryam Waziri da Babangida Tijjani
Auren jarumar Kannywood Maryam Waziri: Ango da amarya sun saki zafafan bidiyon bikinsu | Hoto: Kemi Filani blog
Asali: UGC

Hakazalika Maryam ta yi amfani da shafinta na Instagram don yada albishir da aurenta da tsohon dan wasan kwallon.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumar ta Kannywood ta saka wani kyakkyawan bidiyonta tana sanye da kayan amare yayin da ta fito da wani kwalliyar mai kyau tare da taka rawa a gaban kamera.

Maryam a cikin rubuunta ta yi addu’ar Allah ya kiyaye ta kuma ta ce yanzu kam dai ta shiga daga ciki.

Ta rubuta:

"Allah ka kare ni daga duk wani mai dauka da zai karbe ni daga wanda ya dauke ni...."

Kalli bidiyon ta a kasa:

A bangaren ango, shi ma Tijjani Babangida ya wallafa bidiyoyin bikin auren a shafinsa.

Kalli bidiyon:

Rahotanni sun bayyana cewa Babangida yana daya daga cikin ‘yan kungiyar kwallon Dream Team da suka samu lambar zinare a gasar Olympics ta Atlanta a shekarar 1996.

Martanin masoya

Karanta wasu daga cikin maganganun da magoya keyi bayan samun labarin auren shahararrun ma'aurata:

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Ibraheemgib:

"Allah ya albarka ci gidan aurenku, nji."

Officialmaryambooth:

"Ina taya ki murna 'yar uwa ❤️."

Nusaiberh_jaf:

“AMEEEÉENNN ina taya ki murnar aure qawata ina taya ki farin ciki Allah ya bada zaman lafiya.”

Small_chops_abuja:

“Mashallah, ina taya ki murna 'yar uwa."

Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

A baya, labari da ke bayyana da dumi-duminsa a safiyar Asabar din nan shi ne na auren jarumar shiri mai dogon zango na Labarina.

Mai bayar da umarni na shirin Labarina, Malam Aminu Saira ne ya wallafa bidiyo tare da taya jarumar murnar auren da ta yi a madadin kansa da kamfanin Saira Movies.

Kamar yadda wallafar da @aminusaira yayi ta bayyana:

"A madadi na da kamfanin sairamoviestv, muna taya 'yar uwa Maryam Waziri murnar auren da ta yi a yau, wato Juma'a. Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya ba su zuriya dayyiba. Muna taya ki murna, muna kewar ki Laila"

Kara karanta wannan

Innalillahi: Amarya ta rasu a ranar da aka daura auren ta kafin a kai ta dakin miji

Asali: Legit.ng

Online view pixel