An bindige jami'in gidan yari da wasu mutane 10 a harin gidan yarin Jos

An bindige jami'in gidan yari da wasu mutane 10 a harin gidan yarin Jos

  • 'Yan bindiga sun harbe jami'in gidan gyaran hali da ke Jos a jihar Filato da ke Arewa ta tsaki a Najeriya
  • An ce, an gano gawarwakin wasu mutane da suka mutu yayin da aka kai harin, inda aka gano har da gawar dan bindiga
  • Akalla mutane 11 suka mutu, yayin da daruruwan fursunoni suka tsere daga cibiyar gyaran halin, amma an kamo wasu

Jos, Filato - An harbe daya daga cikin ‘yan bindigar da aka tarfa a cibiyar gyaran hali da ke Jos a ranar Lahadi yayin musayar wuta lokacin da suka kai hari cibiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya (NCoS), Francis Enobore, a wata sanarwa a ranar Litinin ya ce an gano gawar maharin ne a cikin mutane 11 da aka kashe.

Kara karanta wannan

An bayyana adadin mutanen da aka kashe da Fursunonin da suka tsere a harin gidan yari na Jos

Cibiyar gyaran hali ta Jos
An bindige jami'in gidan yari da wasu mutane 10 a harin gidan yarin Jos | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Maharan, wadanda suka kai hari cibiyar da misalin karfe 05:20 na yamma a ranar Lahadi 28 ga watan Nuwamba, 2021, sun yi artabu da jami’in rundunar NCoS da ke dauke da makami a cikin wani kazamin fadan kafin su kutsa cikin farfajiyar gidan.

Vanguard ta ruwaito Enobore na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin takaici, daya daga cikin ma’aikatan NCoS Armed Squad ya riga mu gidan gaskiya a fafatawar yayin da fursunoni 9 su ma suka rasa rayukansu.
"An harbe wani ma'aikaci a hannu sannan kuma fursunoni shida sun jikkata a harin."

Fursunoni 262 ne suka tsere

A halin da ake ciki, wasu daga cikin maharan da jimillar fursunoni 262 ne suka tsere a fafatawar kafin a samu karin jami'ai daga ma'aikatan wata cibiyar.

Sai dai Enobore ya ce kawo yanzu an sake kamo 10 daga cikinsu inda 252 ba a san inda suke ba.

Kara karanta wannan

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

Ya ci gaba da cewa, Kwanturola Janar na hukumar a jihar, Haliru Nababa ya jajantawa ‘yan uwa da abokan jami’in da ya mutu a arangamar, inda ya yi alkawarin cewa bai mutu a banza ba, domin za a farauto duk 'yan ta'addan su fuskanci cikakken fushin doka.

Ya godewa jami’an hukumar da jami’an sauran hukumomin tsaro da suka taimaka wajen shawo kan lamarin, ya kuma ba jama’a tabbacin cewa tsaron fursunonin da suka hada da kulawa da tallafa musu za su ci gaba da zama babban fifiko a hannunsa.

Ya yi kira da a ba da hadin kai daga masu kishin kasa domin kamo fursunonin da suka tsere tare da bayar da sahihan bayanan sirri wadanda za su iya dinke wannan mummunan lamari.

Cibiyar ta Jos a lokacin da aka kai harin tana da fursunoni 1,060 da suka hada da wadanda ake tsare da su 560 kafin a gurfanar da su gaban kuliya da kuma 500 masu laifi.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

A wani labarin, an harbe wasu mutane biyu mazauna kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato yayin da suke fafatawa da masu garkuwa da mutane.

Maharan, a cewar mazauna garin, sun bude wuta kan mutanen da ke bibiyarsu daga maboyarsu. Wasu da dama kuma an ce sun samu raunuka a lamarin.

Wadanda suka mutun dai sun hada da Peter Inyam da Arin Kaze.

Asali: Legit.ng

Online view pixel