Hukumar NCoS ta bayyana adadin mutanen da aka kashe da fursunonin da suka tsere a harin Jos

Hukumar NCoS ta bayyana adadin mutanen da aka kashe da fursunonin da suka tsere a harin Jos

  • Hukumar dake kula da gidan gyaran hali (NCoS) ta bayyana cewa adadin mutum 11 ne suka mutu yayin harin gidan yari a Jos
  • Kakakin hukumar, Francis Enobore, yace jami'in su ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin dogon musayar wuta da maharan
  • Hakanan kuma ya bayyana cewa fursunoni 9 ne suka mutu a harin, yayin da wasu 262 suka tsere

Jos, Plateau - Ɗaya daga cikin yan bindigan da jami'an tsaro suka titsiye a tsakiyar gidan yarin Jos, ya sha alburushi har lahira a fafatawar.

Dailytrust tace kakakin hukumar kula da gidan yari, (NCoS), Francis Enobore, shine ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an gano gawar ɗan bindigan ne a cikin gawarwakin mutum 11 da suka rasa ransu a yayin musayar wutan.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yan bindiga sun faɗa tarkon jami'an tsaro yayin da suka kai hari gidan yari a Jos

Jami'an hukumar NCoS
Hukumar NCoS ta bayyana adadin mutanen da aka kashe da fursunonin da suka tsere a harin Jos Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Maharan sun dira gidan yarin da misalin karfe 5:20 na yamma, inda suka yi musayar wuta da jami'an NCoS kafin su kutsa cikin gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin NCos yace:

"Abin takaicin shine ɗaya daga cikin jami'an kula da gidan gyaran hali ya rasa rayuwarsa a musayar wutan, yayin da fursuna 9 suka mutu."
"Wani jami'i ɗaya ya samu raunin harbi a hannunsa, sannan kuma wasu fursunoni 6 sun jikkata."

Fusunoni nawa ne suka tsere?

Kazalika, hukumar ta bayyana cewa wasu daga cikin maharan da kuma fursunoni 262 sun tsere tun kafin jami'an tsaro su kawo ɗauki.

Enobore ya bayyana cewa tuni jami'ai suka samu nasarar sake damke mutum 10 daga ciki yayin da ake cigaba da neman 252.

Bugu da kari kakakin NCoS yace shugaban hukumar na ƙasa, Haliru Nababa, ya jajantawa iyalan jami'in da ya mutu yayin harin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a ban daki

Ya kuma yi alƙawarin cewa ba zasu bar mutuwarsa ta tafi a banza ba, za'a farauci yan bindigan domin su girbi abinda suka shuka.

Shugaban NCoS ɗin ya kuma gode wa sauran hukumomin tsaro bisa kawo musu ɗauki cikin gaggawa har aka shawo kan lamarin.

A wani labarin na daban kuma Wani Lakcara ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taro, ya rigamu gidan gaskiya

Wani malami a kwalejin fasaha dake Offa jihar Kwara, Ayatu Ikani, ya yanke jiki ya faɗi, kuma ya rasa rayuwarsa daga faruwar haka.

Rahotanni sun bayyana cewa Ayatu na cikin gudanar da taro da mutanensa, yayin da lamarin ya faru da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel