Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi

Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi

  • Wani yaro ya boye cikin injin jirgin sama, kusa da farfela, a yunkurin sa na barin kasarsa zuwa kasar waje
  • Kafin jirgin ya tashi, jami'an tsaro sun gano inda yaron ya boye suka bukaci ya fito daga wurin da ya boye tare da jakarsa
  • Yan Nigeria da dama sun tofa albarkacin bakinsa game da halin da ya shiga har ta sa ya yi ganganci irin wannan

Wani faifan bidiyo da ke nuna wani yaro da jami'an tsaro suka gano shi ya boye cikin injin jirgin sama ya janyo muhawarra a dandalin sada zumunta na zamani.

A cewar Tunde Ednut a shafinsa na Instagram, yaron dan Africa ya matsu ne matuka yana son tafiya kasar waje har ta sa ya jefa rayuwarsa cikin hatsari.

Kara karanta wannan

Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce

Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi
'Yan sanda sun kama wani yaro cikin injin jirgin sama. Hoto: @mazitundeednut
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lallai ya jefa kansa a hatsari

Idan har da jirgin saman ya tashi kuma yaron yana ciki, akwai yiwuwar labarin ya canja domin yana kusa da farfelan jirgin saman da za ta iya masa illa.

A lokacin da jami'an tsaro suka isa wurin, yaron ya fito tare da jakarsa na baya ya kuma sakko daga fiffiken jirgin.

Ga bidiyon nan a kasa:

A lokacin wallafa wannan rahoton, kimanin mutane 2,000 sun tofa albarkacin bakinsu game da lamarin yayin da mutum fiye da 41,000 suka yi 'liking'.

Ya jefa rayuwar kowa cikin hatsari

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutane, ga su nan a kasa:

_pe.ar.l ta ce:

"Toh fa, ban san abin da ya tunzura shi haka ba."

candidusoliver ta ce:

"Fatara ba zabi bane, Ina rokon ka Allah. Ina son in yi murmushi a kowanne bangare na rayuwa na."

Kara karanta wannan

Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa

oluheredotus ya ce:

"Na fi damuwa da yiwuwar injin ta halaka shi wanda hakan na iya janyo gobara a yayin da jirgin ke kokarin tashi. Osinwin eniyan."

pretty_sharon ta ce:

"Kafin jirgin nan ya isa inda zai tafi, yaron nan ma zai mutu ..."

godfirstson_ ya ce:

"Yanzu mai zai faru idan da ba a gan shi ba, da jirgin ya yi hatsari fa."

callme.the.lieutenant ya ce:

"Abin da ya aikata zai iya janyo wa dukkan fasinjojin da ke jirgin su bakunci lahira."

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel