Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa

Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa

  • Wani bawan Alla mai kera akwati gawa ya zama miloniya nan take bayan sayar da wani dutsen samaniya da ya fado a gidansa kan N766 miliyan
  • Joshua Hutagalung yana zaune a gida ne kwatsam sai dutsen mai girmar kwallon kafa ya fado kusa da dakinsa ta rufin gidansa
  • Mahaifin 'ya'ya ukun ya ce yana son ya yi amfani da wani kaso daga kudin da ya sayar da dutsen don gina coci a unguwarsu

Indonesia - Wani bawan Allah ya zama miloniya cikin dare daya bayan wani dutse daga sararin samaniya ya fado gidansa bayan fasa rufin gidan.

Mutumin mai suna Josua Hutagalung dan asalin kasar Indonesia ya sayar da dutsen ga wani kwararren mai sayen kayayyaki kan £1.4 milliyan (N766 miliyan), The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

Mai ƙera akwatin gawa ya zama miloniya a dare guda bayan dutse daga sararin samaniya ya faɗo a gidansa
Bawan Allah ya zama biloniya cikin dare daya bayan dutse daga samaniya ya fado gidansa. Photo Credit: East News Press Agency
Asali: UGC

Yadda abin ya faru

Lamarin ya faru ne a shekarar 2020 a wata rana da Josua ke zaune a gida.

A lokacin da ya ji wani sauti mai ratsa kunne sakamakon fadowar dutsen, Josua ya yi ta tunanin shin menene ya fado duba da cewa ba ruwan sama ake yi ba.

Ya tafi wurin da ya ji karar sai ya tsinci wani dutse mai nauyin kilo gram 2.2 a gidansa.

Kudin da aka biya shi ya kai albashinsa na shekaru 30

Mahaifin 'ya'ya ukun ya wallafa bidiyo a shafinsa na Facebook yana nuna ainihin wurin da dutsen ya fado yana mai cewa dutsen na da zafi a lokacin da ya dauka.

An lissafa cewa kudin da ya sayar da dutsen ya kai albashinsa na shekaru 30.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Mutumin ya ce zai gina wa unguwarsu coci cikin kudin da ya samu bayan sayar da dutsen.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel