Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce

Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce

  • Bidiyon wani mutum da ba a san ko waye ba ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya kayatar da fasinjojin da ke cikin jirgin sama na kasar Uganda
  • A yayin martani kan bidiyon, ministan ayyuka na kasar, Janar Katumba Wamala, ya yi kira ga kamfanin jirgin saman da su dauka matakin ladabtarwa ga ma'aikatan da suka bar tallar fara a jirgin
  • Farar da suka sani da suna Nsenene, ta kasance abu mai soyuwa ga zukatan 'yan kasar Uganda sakamakon yadda suka dauke ta a matsayin abinci mai matukar dadi

Uganda - Bidiyon wani mutum ya na tallar fara a jirgin sama na kasar Uganda kafin ya tashi ya janyo maganganu da yawa a kafafen sada zumunta.

An ga mutumin ya na tallar ga kwastomomi wadanda cike da jin dadi suke ta siyan farar da aka kulla a kananan ledoji yayin da suke mika masa kudi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau

Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce
Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce. Hoto daga @wisdomblogg
Asali: Instagram

Cike da fara'a mutumin ya dinga mu'amala da fasinjojin yayin da ya ke siyar musu da farar.

A bidiyon an gan shi ya na kaiwa da kawowa a cikin jirgin ba tare da ma'aikatan jirgin saman sun hana shi ba.

Ma'aikatan jirgin sama sun shiga matsala

Sai dai, wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun sanar da cewa an dakatar da ma'aikatan jirgin saman daga aiki sakamakon barin mutumin da suka yi yana talla a jirgin saman ba tare da an tsawatar masa ba.

Kamar yadda dan jaridan Uganda, Sudhir Byaruhanga ya sanar, an tuhumi ma'aikatan kan barinsa da suka yi babu takunkumin fuska, ya yi karantsaye ga dokokin kasar na aiki dangane da annobar korona.

Wannan na zuwa ne bayan ministan ayyukan kasar Uganda, Janar Katumba Wamala ya yi kira kan dakatar da dukkan ma'aikatan jirgin a abinda ya kwatanta da rashin da'a.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kama da wuta, mutane da dama sun mutu

"Ina aiki da shugabannin kamfanin jirgin saman kuma idan aka ga wadanda suka bar wannan abun ya faru ya dace a dakatar da su, toh a dakatar da su," Janar Katumba yace.

Fara abinci mai dadi kamar yadda kwastomomin suka nuna

Kamar yadda kwastomomin suka nuna, fara abinci ce mai dadi a Uganda. Fara wacce mazauna can ke kira da Nsenene ana soya ta kuma har a gwangwani ake sanya ta ana siyarwa a manyan kantunan kasar.

Ana yawan samun fara a lokacin damina cikin watannin Afrilu, Mayu, Yuli, Oktoba da Nuwamba. Hada su kuwa tare da soyata ba wani abu bane mai wuya. Ana cire fiffike da cinyoyin daban kafin a wanke, ta bushe sannan a soya. Ba a amfani da man gyada mai yawa wurin suyar.

Jama'ar kasar na matukar cin Nsenene kamar yadda suke kiran ta sakamakon sinadaran Vitamin A,B da C da take da shi. Ta na da sinadarin protein fiye da madara da kifi. Ta na samar da karfi fiye da alkama.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Kafafen sada zumuntar zamani sun yi martani

@vetsola cewa tayi: "Afrika wa ye ya la'ance ki?'
@isibor_eris ta ce: "Kai cikin jirgin saman ma kamar tashar mota ta Oshodi."
@diana_Ben_dxb cewa tayi: "Wahalah".

Asali: Legit.ng

Online view pixel