Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

  • Abubakar Malami, ministan shari'a, ya sanar da cewa gwamnati ta shirya tsaf wurin mitsike 'yan bindiga bayan kotu ta ayyana su da 'yan ta'adda
  • Kamar yadda takardar da ya fitar tace, wannan jiran da gwamnatin tarayya da ma'aikatar shari'a ta yi har kotu ta yi hukunci, ya na nuna biyayyarsu
  • Malami ya ce, sun yi biyayya ga dokokin duniya wurin daukar mataki tare da shawo kan ta'addanci a kasar nan

Abuja - Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya ce gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin mitsike 'yan bindiga saboda kotu ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda wanda ofishinsa ya mika da bukatar gaban kotun.

Dr. Umar Jibrilu Gwandu, mai bada shawara na musamman a ofishin antoni janar din ya sanar da hakan ta wata takarda da ya fitar ga manema labarai, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda
Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda takardar tace, ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda alamu ne na shirin ofishin antoni janar na tarayya da kuma gwamnatin tarayya na ganin bayansu amma cike da bin doka.

"Wannan cigaban ya bayyana mayar da hankali da gwamnatin tarayya ta yi wurin kiyaye dokokin duniya tare da mutunta su wurin yakar ta'addanci, kungiyoyin ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wannan abu na nuna cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka babban mataki wurin magance matsalar kungiyoyin ta'addanci da masu daukar nauyinsu domin kawo karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.

"Ofishin antoni janar kuma ministan shari'a tare da hadin guiwar cibiyoyin gwamnati da lamarin ya shafa har da jami'an tsaro suna aiki ba dare ba rana wurin yin amfani da wannan sabon hukunci.
"Gwamnati za ta buga a jarida kuma za ta yayata wannan dokar," takardar tace.

Kara karanta wannan

Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsa da makamansu, COAS ga dakarun soji

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

A wani labari na daban, babban kotun tarayya ta Abuja ta bayyana kungiyoyin `yan bindiga da ke barna a fadin kasar nan a matsayin 'yan ta'addan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mohammad Abubukar, daraktan gurfanarwa (DPP) a ma'aikatar shari'a wanda ya shigar da karar, yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ya dauka,wanda babban dalilin hakan shine ganin bayan kungiyoyin `yan bindiga da `yan ta'adda da sauran kungiyoyin ta'addanci a kasar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel