Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsu da makamansu, COAS ga dakarun soji

Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsu da makamansu, COAS ga dakarun soji

  • Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya umarci sojoji da su halaka 'yan bindiga da 'yan ta'addan fadin kasar nan
  • Ya umarci sojojin da su zage damtse wurin ganin bayan 'yan ta'adda, bayan sun kashe su, su kawo gawawwakinsu tare da makamansu
  • Janar Faruk ya yi kira ga jama'a da su baiwa dakarun goyon baya wurin samar musu da bayanan da za su taimake su wurin ganin bayan miyagu

Minna, Niger - Shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su bindige 'yan bindiga da 'yan ta'adda tare da kawo gawawwakinsu da makamansu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya bayar da wannan umarnin ne a yayin ziyarar da ya kai wa birged ta 31 ta horarwa, TRADOC da ke Minna inda ya kaddamar da rukunin dakunan kwanan hafsoshin sojoji matafiya a ranar Lahadi.

Read also

Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa

Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsa da makamansu, COAS ga dakarun soji
Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsa da makamansu, COAS ga dakarun soji. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC
"Na zo Niger a yau ne a cikin wani ziyarar aiki na 31 Artillery Brigade da TRADOC. Na jinjinawa dakarun kan ayyukan da suke yi. Kada ku sassauta, ku cigaba kuma kada ku sassauta wa 'yan ta'adda.
"Idan muka yi arangama da 'yan ta'adda da 'yan bindiga, mu kashe su kuma mu kawo gawawwakinsu da makamansu kuma mu cigaba da yin hakan," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce rundunar za ta cigaba da karfafa guiwar sojojin ta hanyar samar musu da dukkan goyon bayan da suke bukata domin su samar da tsaro a jihar da Najeriya baki daya, Daily Trust ta ruwaito.

Laftanal Janar Yahaya ya ce wannan ziyarar ta ba shi damar tattaunawa kai tsaye da sojojin tare da sanin kalubalen da suka fuskanta da kuma karfafa musu guiwa wurin yi wa kasar nan aiki.

Read also

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

Ya yi kira ga jama'a da su samarwa da rundunar sojin goyon baya da sauran hukumomin tsaro ta hanyar basu bayanan da za su basu damar ganin bayan 'yan ta'adda.

"Na yi kira gare ku da ku bada goyon baya ta hanyar samar da bayanai ga rundunar soji da sauran hukumomin tsaro.
"Wadannan 'yan ta'addan, da yawa daga cikinsu suna rayuwa tare da mu. Ina son jama'a su bayar da hadin kai kuma su dauka tsaro a matsayin matsalar kowa. Da hadin kai ne kawai za mu iya inganta tsaro," yace.

Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa

A wani labari na daban, Shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya jinjinawa runduna ta 25 ta Operation Hadin Kai kan yadda suka fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Read also

Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka

Daily Trust ta ruwaito cewa, murna tare da shagali sun barke a Damboa bayan sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda da suka kai farmaki garin wurin karfe 6:35 na safiyar Juma'a.

Tabbas wannan ya kawo tashin hankali ga mazauna yankin amma dakarun sojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan, lamarin da yasa suka tsere tare da barin garin.

Source: Legit.ng

Online view pixel