Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

  • Mammalakan gidajen mai a Najeriya sun bayyana cewa suna maraba da shirin cire tallafin man fetur
  • Shugaban kungiyar IPMAN ya bayyana cewa wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka shine daidai
  • "Abinda muke so shine ayi daidaito wajen baiwa kowa yanin sayar da hajarsa yadda ya so idan aka cire tallafin," ya kara.

Legas - Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu IPMAN sun bayyana cewa tana maraba da shirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya zata yi a 2022.

Shugaban kungiyar, Mr Chinedu Okoronkwo, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma'a a jihar Legas.

Mr Okoronkwo, ya bayyana cewa ai tun ranar 16 ga Agusta, 2021 Shugaban kasa ya soke tallafin mai tun da ya rattafa hannu kan sabuwar dokar PIA.

Kara karanta wannan

Cire tallafin mai da biyan N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Ahmed Adamu

Yan kasuwan Mai IPMAN
Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN Hoto: OANDO
Asali: UGC

A cewarsa:

"Mu a matsayinmu na yan kasuwa mun dade muna baiwa Gwamnati shawarar cire tallafin mai saboda babu amfani ga cigaba."
"Muna maraba da wannan shawara na daina biyan tallafi a 2022 kuma muna sa ran cewa hakan zai janyo hankulan masu zuba jari."
"Abinda muke so shine ayi daidaito wajen baiwa kowa yanin sayar da hajarsa yadda ya so idan aka cire tallafin."

Ya shawarci gwamnati da ta yi amfani da kudin da take biyan tallafin wajen wasu abubuwan alfanu ga mutane irinsu kiwon lafiya, ilimi, aikin noma dss.

Cire tallafin mai da biyan yan Najeriya N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Adamu

Malami a jami'ar Nile dake birnin tarayya Abuja, wanda yayi takhassusi a sashen tattalin arzikin man fetur Masani , Dr Ahmad Adamu ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

A hirar da yayi da wakilin Legit Hausa, Dr Adamu ya yi alhinin shirin da gwamnatin tarayya ke yi na cire tallafin mai a irin wannan lokaci.

A cewar Malamin, gwamnatin Buhari tun lokacin da ta hau mulki a 2015 take kame-kame game da lamarin tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel