Bamu ji motsin kowa ba har yanzu, Matar dan a mutun Buhari da aka kashe a jihar Anambra

Bamu ji motsin kowa ba har yanzu, Matar dan a mutun Buhari da aka kashe a jihar Anambra

  • Wasu matasa a jihar Anambra sun hallaka dan a mutun Buhari, Kenechukwu Okeke, a gidansa dake Npkor
  • Matar marigayin ta bayyana cewa Gwamnatin nan da yan fafutuka sun yi watsi da iyalinta tun bayan kisarsa
  • Kenechukwu Okeke ne wanda yayi fito-na-fito da wadanda suka yi zanga-zangar EndSARS inda ya kaisu kotu

Jihar Anambra - Iyalan dan a mutun Shugaba Muhammadu Buhari, Kenechukwu Okeke, sun yi kira ga Gwamnati ta kwato musu hakkinsu kan kashe dansu da wasu matasa sukayi a Nkpor.

Matar marigayin ta bayyana cewa wani mutum wanda ya zauna gidansu a baya ne ya kashe mata miji.

An ruwaito cewa wasu matasa bakwai sun sassareshi kuma suka banka masa wuta har lahira a gaban matarsa Mrs. Blessing Odinakachi Okeke.

Wannan abu ya auku ne tun watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

Matar marigayin ta bayyanawa Thisday cewa Gwamnatin nan da yan fafutuka sun yi watsi da iyalinta tun bayan kisarsa kuma har yanzu ba'a kama wanda ya kasheshi ba.

A cewarsa:

"Wani tsohon mai zama a gidanmu, Chiadiobi, ne ya kashe Kenechukwu Okeke. A baya ya zauna a gidanmu amma ya kashe kayansa ba tare da sanar da kowa ba kuma ya bukaci a bashi kudin watanni biyu da ya rage cikin hayarsa, sai muka ce ba zamu bashi ba tunda bai sanar da mu zai tashi ba."
"Ya yi barazanar cewa zai koya mana darasi. Wani zubin zai shigo gidan ya balla kofa kuma ya dauki abinda ya so."
"Wata rana ya shigo gidan kuma mijina ya fuskancesa, ashe akwai wasu matasa tare da shi, kawai sai suka fara saransa kuma suka zuba masa man janareto suka banka masa wuta, haka mijina ya mutu."

Kara karanta wannan

Kada ku damu zan biya kudin sadaki, Bokanya na rokan maza su zo su aureta

An bankawa gawarsa wuta
An kashe wani dan a mutun Buhari a jihar Anambra, an bankawa gawarsa wuta Hoto: Thisday Newspaper
Asali: Facebook

Har yanzu ba'a kama wanda yayi haka ba kuma babu taimako daga kowa

Mrs Okeke tayi alhinin yadda tun kisan mijinta babu wanda ya tuntubesu don daukar nauyin birneshi.

Tace abinda yafi bata mata rai shine wanda ya kashe mijin har yanzu yana yawonsa a gari yana alfahari da abinda yayi.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenganyia, ya bayyana cewa hukumar na gudanar da bincike kan lamarin.

"An kawo kara amma gaskiyar itace babu isasshen bayanai har yanzu. Ku bani dan lokaci," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel