Kada ku damu zan biya kudin sadaki, Bokanya na rokan maza su zo su aureta

Kada ku damu zan biya kudin sadaki, Bokanya na rokan maza su zo su aureta

  • Watan yar addinin gargajiya a jihar Enugu ta yi kira ga mazaje masu neman aure amma basu da kudi su garzayo wajenta
  • Amara tayi kira ga mazaje su ribaci wannan dama saboda ita kyakkyawar mace ce kuma bata bukatar kudi

Enugu - Wata bokanya wacce tayi ikirarin mika rayuwarta ga Shaidan na neman mijin aure ido rufe nan zuwa karshen shekarar 2021.

Bokanyar mai suna Precious Gift Amarachi ta bayyana cewa duk namijin da ya amince da aurenta, kada ya damu da kudin sadaki, ita da kanta zata biya.

Precious tace amma wannan daurin aure a wajen bautarta za'ayi cikin ruwa.

Kada ku damu zan biya kudin sadaki
Kada ku damu zan biya kudin sadaki, Bokanya na rokan maza su zo su aureta Hoto: Precious Gift Amarachi
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

‘Yan bindiga sun sake kai hari Filato, sun kashe mutane biyu

A jawabin da ta sake a shafinta na Facebook, Precus Amara ya bayyana cewa samari masu neman aure sun ribaci wannan dama saboda ita kyakkyawa ce.

A cewarta,

"Idan kai saurayi ne mai neman matar aure wannan Disamban kuma ba kada kudi, kada ka damu gani nan."
"Zan biya kudin sadakin da dukkan abubuwan da ake bukata da sharadin za'ayi auren a wajen bauta na."
"Nice wannan kyakkyawar budurwar da ta mika zuciyarta ga Shaidan."

Mutane sun tofa albarkatun bakinsu:

Sani Baba Ahmad yace:

Wannan sai su Okonkwo

Nuraddeen Mannir yace:

Ubanwa zai aureki a wajen kwanciya ki barbaɗawa mutum magani Jela ta ƙyame.

Suleman Suleman yace:

Ganinan zuwa yanzu wannan shine tsuntsu daga sama gashashe

Muhammad Sani Gusau yace:

Toh miji har nawa zata aure ni??

Khalid Hassan Abubakar:

A hakanne kyakkyawan?
Waze auri bokanya karaba

Itz Basheer Umarr

Read also

Mata ta sheke mijinta kwanaki bayan 'yar uwarta ta kashe nata

To bada ni ba gada a hurumi
Muhammad Aliyu Gidado
To Ita kuma maza nawa zata aura kenan...??

Auwal Umar:

Baki iya danbo ba,,,,,,

Aisha Abdulhamid:

Amma baku da hankali ina ruwan mu da wanga useless news din yanzu anfanin me zai mana please a barmu muje da daya

Source: Legit.ng

Online view pixel