Abin da ya sa Gwamnati ba ta isa ta rabawa Talakawa kudi idan an cire tallafi ba - Majalisa

Abin da ya sa Gwamnati ba ta isa ta rabawa Talakawa kudi idan an cire tallafi ba - Majalisa

  • Majalisar Dattawa tace ba a ware kudin za a rabawa talaka idan an cire tallafin man fetur a 2022 ba
  • Shugaban kwamitin tattalin arziki, Sanata Adeola Olamilekan Solomon, ya bayyana haka dazu a Abuja
  • Adeola Solomon yace dole sai an kawo takarda gaban majalisa kafin gwamnati ta iya kashe N2.4tr

Abuja - Kwamitin tattalin arziki na majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa babu inda aka ware N5000 domin marasa karfi a kasafin shekarar 2022.

Majalisar dattawan kasar tace a kasafin kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar kwanan nan, babu inda aka ware wadannan makudan kudi.

Daily Trust ta rahoto shugaban kwamitin, Adeola Olamilekan Solomon yana wannan bayani da ya zanta da manema labarai a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2021.

Sanata Adeola Olamilekan Solomon ya yi magana da kwamitinsa ya gabatar da rahoton aikinsu gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa yau a Abuja.

Kara karanta wannan

Kada ku damu zan biya kudin sadaki, Bokanya na rokan maza su zo su aureta

Sanata yace kafin gwamnatin tarayya ta iya kashe kudi masu yawa haka a gwamnatance, dole a ware masu kaso na musamman a kasafin kudin shekarar badi.

Majalisa
Zauren Majalisa Hoto: Tope Brown / @NgrSenate
Asali: Facebook

“Ba na so in je ga batun yanzu. Na yi imani kafin a amince da wannan, dole a kawo takarda zuwa majalisar tarayya domin mu ga yadda za ayi.” – Solomon.
“Babu wani wuri da yake nuna ‘yan Najeriya za su rika karbar N5000 a duk wata a matsayin alawus na zirga-zirga, wanda har za a kashe Naira tiriliyan 2.4”

Sai majalisa ta ga yadda za ayi - Kwamiti

‘Dan majalisar yace aikin majalisa ne ta zauna ta ga hanyar da za a bi wajen gano mutane miliyan 40 da za a raba wadannan kudi da Ministar kudin ta ke magana.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta gano N4.5bn na aikin barikin 'yan sanda a cikin kasafin NDLEA

Tribune ta rahoto Sanatan ya na mamakin ta inda wannan makudan kudi da ake nema za su fito, ganin ana kukan kudin da ake samu daga danyen mai ya yi kasa.

“Shiyasa na ce har yanzu surutu ne kurum, har sai an kawo mana kudiri a majalisar tarayya a matsayin cikin kasafin kudi, ko ayi wa kundin kwaskwarima.”

Hakan na zuwa ne bayan Ministar tattali, kasafi da tsare-tsaren arziki, Zainab Ahmed tace za a ware kudin da za a rika rabawa talaka domin suyi zirga-zirga.

A cire tallafin fetur, kara haraji, rage cin bashi

A yau ne mu ka tattaro maku duka jerin shawarwarin da masanan bankin Duniya su ka ba Najeriya domin a iya ceto tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2022.

Bankin Duniya ya bukaci a bude iyakokin kasa domin kaya su shigo, sannan a rage cin bashi, kuma a kashe tallafin fetur da nufin farfado da tattalin arzikin kasar

Kara karanta wannan

Shirin karin farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

Asali: Legit.ng

Online view pixel