Ba karamin kaunarta nike ba, Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70

Ba karamin kaunarta nike ba, Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70

  • Matashi mai suna Bernard Musyokiya bayyana irin mahaukacin son da yake yiwa matarsa Deborah Jan
  • Bernard Musyokiya dai dan shekara 35 yayinda sabuwar amaryarsa kuwa yar shekara 70 ce kuma tana da 'yaya biyu
  • Matashin ya bayyana cewa ya kosa su sheka kasar Amurka inda zai kasance tare da ita kadai su sha soyayyarsu
  • Deborah da sabon Angon a Facebook suka hadu

Matashi dan kasar Kenya, Bernard Musyokiya, ya auri Ba-Amurkiya yar shekara 75 Deborah Jan.

Matashin ya jaddada cewa shi fa soyayyar gaskiya yake mata kuma ba don kudi yake ba kamar yadda ake radawa.

Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70
Ba karamin kaunarta nike ba, Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70 Hoto: Bernard Musyoki
Source: UGC

Read also

'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita

Yadda suka hadu

Musyoki, wanda dan jihar Kitui ne a Kenya ya bayyanawa jaridar TUKO.co.ke cewa ya hadu da Deborah ne a manhajar Facebook a shekarar 2017.

A cewarsa:

"Ni na bukaci mu fara kawance, bayan mako guda, nace mata ta aure ni kuma ta amince."

A 2018, Musoyoki yace ya shirya zuwa Amurka don haduwa da ita amma aka hanashi biza amma bai yanke tsammani ba.

Ya ce a 2020 ya sake neman biza kuma aka sake hanashi.

Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70
Ba karamin kaunarta nike ba, Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70 Hoto:Hoto: Bernard Musyoki
Source: UGC

Bamu daina tattaunawa ba

Yace basu daina tattaunawa da juna ba har karshen Disamban 2020, matar ta yanke shawaran zuwa Kenya domin haduwa da shi.

Yace:

"Muna bacci a dakuna daban-daban kuma mun yi alkawarin ba zamu yi jima'i ba har sai an daura mana aure."

A ranar 2 ga Febrairu, 2021, aka daura musu aure a Sheria kuma mutane suka shaida.

Ya ce 'yan uwansa sun yi mamaki lokacin da yace zai auri Deborah.

Read also

Mutane sun tarawa mutumin da ya kwashe shekaru 43 cikin kurkuku kudi, N95m, bayan an gano sharri akayi masa

Yan Najeriya sun yi tsokaci:

Fatima Ta Annabi tace:

"Talauci masifane wannn ai iyace sa'ar kakarshi,Allah yakyauta."

Æthëærmu Prësdœr:

Hhhhhh to wlh Koni yadda nake Shan luguden wahala a Nigeria dana samu wacce zatayi wup Dani wallah Ina fecewa

Zainab Yusuf tace:

Hmmmm... Ba dole yaso taba, ita ba dole tasoshi ba, Abar kaza cikin gashin ta kawai..

Hauwau Muhammad tace:

Kamar na dankara ashar wallah Wai soyayya nabi soyayya da Dan banzan guda na daushi keyar ta da katako tirrrrr

Salisu Nasiru yace:

Karya yake shege, kudi yabi, tsohuwa saar kakarsa zaice wani yana mugun sonta

Source: Legit.ng

Online view pixel