Tserewa zan yi zuwa Amurka bayan cikar wa'adin mulki na, Obiano ga EFCC

Tserewa zan yi zuwa Amurka bayan cikar wa'adin mulki na, Obiano ga EFCC

  • Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya sanar da hukumar EFCC cewa Amurka zai koma da zama idan ya kammala mulkinsa
  • Gwamnan ya sanar da hakan ne a matsayin martaninsa ga hukumar bayan sanarwar da ta fitar na cewa idon ta na sanye kan sa
  • Hukumar EFCC ta aike wa da shugaban hukumar shige da fice ta kasa cewa tana da bukatar sanin kaiwa da kawowar gwamnan Anambran

Anambra - Gwamna Willie Obaino na jihar Anambra ya ce zai koma zama Amurka bayan cikar wa'adin mulkinsa na gwamnan jihar.

Obiano zai mika mulki hannun Farfesa Chukwuma Soludo a ranar 17 ga watan Maris na shekara mai zuwa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Tserewa zan yi zuwa Amurka bayan cikar wa'adin mulki na, Obiano ga EFCC
Tserewa zan yi zuwa Amurka bayan cikar wa'adin mulki na, Obiano ga EFCC. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Amma kuma hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta saka sunan gwamnan cikin wadanda ta ke nema.

Read also

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

A wata wasika da hukumar yaki da rashawa ta aike wa hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, ta ce a sanya wa kaiwa da kawowar Obiano ido, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wasikar da aka aike zuwa shugaban hukumar, EFCC ta bukaci a sanar da ita duk lokacin da Obiano zai bar kasar nan zuwa wata kasa daban kuma a sanar mata da filin jirgin da zai tashi da kuma inda zai sauka.

Amma kuma a yayin martani a madadin gwamnan, kwamishinan yada labarai da hulda da jama'a na jihar, Don Adinuba, ya zargi EFCC da yin aiki da sakon wasu.

Ya ce a halin yanzu watanni hudu kacal suka rage wa Obiano a ofishinsa kuma hukumar har ta samu damar zuwa ta bayyana cewa ta na bincikarsa.

Read also

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Adinuba ya ce gwamnan ya sanar da cewa ya na kammala wa'adin mulkinsa zai koma Amurka da zama.

EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

A wani labari na daban, hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sanya Willie Obiano, gwamnan Anambra a cikin jerin sunayen wadanda take sa ido a kai.

Wannan batu ya zo ne watanni kafin Obiano ya bar ofis a matsayin gwamnan Anambra, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

A cewar wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Nuwamba kuma zuwa ga kwanturola-janar na hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), hukumar EFCC ta bukaci a sanar da ita duk lokacin da aka ga Obiano na yunkurin fita kasar waje.

Source: Legit

Online view pixel