Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

  • Babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, ta haramta wa EFCC gurfanar da tsohon gwamnan jihar Seriake Dickson
  • Kamar yadda EFCC ta bayyana, ta samu korafi kan cewa sanatan a halin yanzu ya yi rub da ciki kan N1 tiriliyan na jihar yayin da ya ke gwamna
  • Sai dai Mai Shari'a Isah Dashien ya sanar da cewa, dukkan dukiyar sanatan ta samu tantancewa daga CCB kuma akwai shaidar hakan

Yenagoa, Bayelsa - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa, jihar Bayelsa, ta bada umarnin haramta wa hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa daga gurfanar da Seriake Dickson, tsohon gwamnan jihar Bayelsa.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, a watan Augustan da ya gabata, EFCC ta titsiye sanatan da ke wakiltar Bayelsa ta kudu na sa'o'i kan zarginsa da rashawa tare da amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa
Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ana zargin Dickson da watanda da kudi har N1 tiriliyan yayin da ya ke gwamnan jiharsa, zargin da ya musanta. Ya ce korafin da aka mika gaban hukumar duk sharri ne, TheCable ta ruwaito.

"Domin gujewa tantama, ina son in sanar da cewa hannaye jarin iyalaina, Seriake Dickson Trust Incorporated an kafa su ne tsakanin 1996 zuwa 2012 kafin in zama gwamna," Dan majalisar yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wadannan hannayen jarin an same su ne ta hanyar cin bashi wanda na ke biya daga albashi, alawus da sauransu. A halin yanzu daya daga cikinsu ban gama biya ba kuma na baiwa EFCC takardun."

A hukuncinsa, Alkali Isah Dashien ya tsaya kan cewa an samu kadarorin ta hanyar bashi ne wanda kuma CCB ta tabbatar.

"A don hakan, wannan lamari ya ci karo da dokar EFCC na bincike a bayyana kan kadarori wadanda a shekarun baya aka bayyana halascinsu kuma CCN ta bayar da takardar tantancewa," Dashien yace.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da mataimakin ma’ajin jami’ar Ahmadu Bello, Iliyasu Abdulrauf Bello gaban alkali Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna bisa zarginsa da kwasar N6,000,000.

Iliyasu na rike da kujerar mukaddashin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’ar, SSANU, reshen jami’ar. Ana zarginsa da wawurar wasu kudade daga asusun kungiyar da aka ware don walwalar ma’aikatan.

Bincike ya nuna yadda aka dinga wawurar kudade daga cikin asusun kungiyar ba tare da mambobin kungiyar sun sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel