Da dumi-dumi: Sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kamfanin man fetur a jihar Ribas

Da dumi-dumi: Sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kamfanin man fetur a jihar Ribas

  • Wata sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kan wani kamfanin man fetur a jihar Ribas ranar Laraba
  • Harin na zuwa ne bayan da kungiyar tsagerun suka ba kamfanin man fetur din wa'adin sa'o'i 24 don biya musu bukatunsu
  • Kungiyar ta bayyana irin rashin jin dadinta kan batutuwan da suka shafi hulda da jama'ar yankin da kamfanin

Ribas - Wata sabuwar kungiyar ‘yan bindiga a jihar Ribas mai suna ‘Bayan-Men’ ta sake kai hari a wani kamfanin mai na Nigeria Agip Oil a unguwar Obosi a Omoku, karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni.

Harin ya biyo bayan cikar wa'adin sa'o'i 24 da mayakan suka baiwa kamfanin domin biyan musu bukatunsu.

Taswirar jihar Ribas
Da dumi-dumi: Tsageru sun kai hari kamfanin man fetur a karo na biyu a Ribas | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Punch ta tattaro cewa sabon harin ya haifar da fashewar wani abu da ya wargaza nutsuwar yankin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Janar Agaba na kungiyar 'Bayan-Men', ta bayyana cewa, za ta kara kai hare-hare a kan cibiyoyin Agip, idan har kamfanin bai ja da baya ba tare da shiga cikin al’ummar Omoku kai tsaye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta ruwaito Agaba a cikin sanarwar yana cewa:

"Wannan matakin da muka dauka ya biyo bayan gazawar Agip na kin bin wa'adin sa'o'i 24 da muka ba su domin su jawo hankalin jama'ar mu kan yadda za su fara hulda da jama'a kai tsaye fiye da ta hanyar daidaikun mutane.
“Mu ba 'yan ta'adda bane, mu ’yan boko ne. Gaskiyar ita ce, idan aka tura mutum bango, yakan dawo baya da karfi.
“Muna ba Agip karin kwanaki bakwai ta bude tagogin tattaunawa da al’ummomi 27 na kabilar Omoku.
“Wannan taron zai hada da sarakunan wadannan al’ummomin, da CDC (Community Development Committee) shugabannin al’umma da kuma shugabannin matasa na al’ummomi 27. Haka muke so.
"Ba ma son haka a zauren kowa, muna son ayi a Cibiyar Jama'a inda kowa zai zo.

“Dalilin da ya sa muke son sassauta lamarin a yanzu shi ne saboda kararraki daga bangarori daban-daban da kuma bikin mu na Nchaka da ke tafe a ranar Lahadi.
"Ba ma son wani abu ya shafi bikinmu."

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

A wani labarin, an kashe wani malamin jami'a mai suna Ahmed Saheed da dalibin digiri dan aji daya a Kwalejin Ilimin Kiwon Lafiya ta Farko ta Michael Otedola (MOCPED) da ke karamar Hukumar Epe a Jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An ce an kashe malamin ne a kusa da garin Poka da ke Epe, yayin da dalibin mai suna Razak Bakare kuma aka harbe shi a harabar jami’ar.

Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Daily Trust cewa, lamurran masu ban takaici, sun faru ne cikin sa’o’i 48.

Asali: Legit.ng

Online view pixel