Bilicin: Jarumar fim ta caccaki ‘yan mata da ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

Bilicin: Jarumar fim ta caccaki ‘yan mata da ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

  • Jarumar nan ta masana'antar shirya fina-finan kudu, Nollywood, Shan George, ta yi shagube ga 'yan matan da ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu
  • Shan George ta nuna al'ajabi a kan ribar da masu bilicin ke samu a rayuwarsu
  • Ta bayyana cewa duk da bilicin din da suke hakan bai sa sun samu mijin aure ko kuma a ga sun yi kudi ko samun wani matsayi na musamman ba

Shahararriyar jarumar nan ta masana'antar shirya fina-finan kudu, Nollywood, Shan George, ta caccaki 'yan matan da ke shafe-shafe domin sauya launin fatarsu wato bilicin.

A wani wallafa da tayi a shafinta na Instagram, jarumar ta tambayi mata masu bilicin kan ribar da suke samu a shafe-shafen da suke yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kamfanin man fetur a jihar Ribas

Jarumar fim ta caccaki ‘yan mata da ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu
Jarumar fim ta caccaki ‘yan mata da ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu Hoto: Instagram shangeorgefilms/allnews.ng
Asali: UGC

Jarumar wacce ke da hasken fata ta bayyana rashin amfanin da ke tattare da sauya launin fata.

Shan George ta ce:

"Bayan duk wani shafe-shafe na bilicin, yanzu ga shi kin yi fari fau har muna iya ganin jijiyoyin jikinki da kalolin kore da ja, har yanzu baki samu mijin aure ba, baki yi kudi ba, kuma baki samu karramawa ko digirgir ba. Menene ribar ki?"

Babban dalilin da yasa mutane ke shafe-shafe don sauya launin fatarsu

A gefe guda, mun kawo a baya cewa hakika babu wanda ya ke daukar wani mataki a rayuwar sa ba tare da wani kakkwaran dalili ba. Don haka har masu sauya launin fatar su su na da manyan dalilan yin hakan.

An taba kiran ka da bilaki? Duna na lillahi? Dan baki ko kuma ‘yar baka? Saboda launin fatar ka ta na da duhu? Yayin da ake kiran wasu fararen da bature, Dan fari da sauran su.

Kara karanta wannan

Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci

Bisa ruwayar Daily Trust, ya kamata a matsayin mu na ‘yan Najeriya, mu rungumi bakaken fatocin mu kuma mu dena amfani da kalaman nan don su kan yi tasiri a zukatan wadanda ake furta ma wa.

Duk da illolin bilicin, Daily Trust ta bayyana yadda ya karade ko ina. Yanzu haka kamfanonin mayukan bilicin su na matukar ciniki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel