Bayanan Sirri: Boko Haram ne ke kai hare-haren babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

Bayanan Sirri: Boko Haram ne ke kai hare-haren babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

  • Bincike ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram ne suke kai harin da ake yawan kai wa matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna
  • A ranar Lahadi, wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da matafiya da dama sannan suka halaka wani fitaccen dan siyasan jihar Zamfara a hanyar Kaduna
  • Washegari ‘yan bindigan sun kara komawa kusa da inda suka kai harin suka bude wa matafiya wuta sannan suka kara sace wasu

Kaduna - Bincike ya bayyana cewa hare-haren da ake yawan kai wa babban titin Abuja zuwa Kaduna duk ‘yan Boko Haram ne suke kai farmakin, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba sannan sun halaka wani fitaccen dan siyasan jihar Zamfara, Sagir Hamidu a wani wuri mai suna Kurmin Kare a kan hanyar.

Read also

Zamfara: 'Yan bindiga sun saka wa mutane haraji, sun ce wanda bai biya ba zai yaba wa aya zaƙin ta

Bayanan Sirri: Boko Haram ne ke kai hare-haren babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
Bayanan Sirri: Boko Haram ne ke kai hare-haren babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

‘Yan ta’addan sun kara komawa kusa da wurin sannan suka kara budewa wasu matafiya wuta har suka yi garkuwa da wasu.

Masu bayar da bayanan sirri a Abuja sun bayyana wa Daily Nigerian cewa, duk ‘yan Boko Haram ne suka kafa sansani a dajikan Kaduna da na Neja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

“Bisa bayanan sirri, an gano cewa ‘yan Boko ne suke da alhakin kai farmaki a wuraren Kurmin Kare dake kan babban titin Abuja zuwa Kaduna.
“Su ne suke satar mutane a wuraren Mashegy da Shiroro a jihar Neja. Suna kokarin ganin sun taru a yankin ne don garkuwa da mutane tare da tara kudade masu tarin yawa.
“Sun kafa sansanoninsu a Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da sauran wurare. Kuma su na ci gaba da zagaye wuraren kilomita 50 zuwa 60 daga babban titin Abuja zuwa Kaduna.”

Read also

Gwamnatin Neja ta koka, tace ‘Yan Boko Haram su na hana iyaye kai yaransu makaranta

“Daga wuraren, suna amfani da babura don yawace-yawace. Akwai karamar hanya da suke ajiye baburansu sannan su karasa tafiya a kafa har cikin dazukan da suke zama,” a cewar majiyar.

Yace jami’an tsaro ciki har da gwamnatin jihar Neja da ta jihar Kaduna sun gano yadda lamarin yake ci gaba da lalacewa da kawo karshen rashin tsaron.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a yanzu ‘yan Boko Haram ne suke garkuwa da mutane kuma suna yin aiki ne tare da hadin kan ‘yan bindiga.

An kasa samun Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige har lokacin rubuta wannan rahoto.

Bayan harin Lahadi, yan bindiga sun sake sace mutane ranar Litinin a titin Kaduna/Abuja

A wani labari na daban, tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya karo na biyu a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2021.

Read also

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Daily Nigerian ta ruwaito cewa yan bindigan sun farmaki matafiya ne misalin karfe 4:30 na yamma kuma suka budewa matafiyan wuta.

Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa kusan waje daya aka tare matafiya ranar Litinin da Lahadi.

Source: Legit.ng

Online view pixel