Gwamnatin Neja ta koka, tace ‘Yan Boko Haram su na hana iyaye kai yaransu makaranta

Gwamnatin Neja ta koka, tace ‘Yan Boko Haram su na hana iyaye kai yaransu makaranta

  • ‘Yan ta’addan Boko Haram su na shiga wasu kauyukan da ke jihar Neja suna yin kira ga al’umma
  • Gwamnatin Neja ta ce Boko Haram ta na fadawa iyaye su daina kai ‘ya ‘yansu makarantun boko
  • Ahmed Ibrahim Matane yace sojojin Boko Haram da na ISWAP sun addabi wasu yankuna a Neja

Nigeria - ‘Yan ta’addan Boko Haram da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja, su na matsawa iyaye a kan su cire ‘ya ‘yansu daga makarantun boko.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan ta’addan su na kuma kokarin sa iyaye su bijirewa umarnin gwamnati, tare da karbar haraji daga hannun al’umma.

Kungiyar Boko Haram su na kona gonakin duk wanda ya ki biyan kudin da aka daura a wuyansa.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana wannan da ya zanta da ‘yan jarida jiya, a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, 2021.

Read also

ISWAP na ƙokarin kafa daular ta a Jihar Neja, Gwamnatin jiha

Alhaji Ahmed Ibrahim Matane yace baya ga haka ana fama da garkuwa da mutane a yankunan Kwaki, Kusaso, Kawure, Chikuba, Kurebe, da kuma Madaka.

Jaridar The Cable ta rahoto Matana yana cewa an sace mutane a Farin-Dutse, Falali da Ibbru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan Boko Haram
Sojojin Najeriya Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

Jawabin Sakataren gwamnatin Neja

“Wadannan ne wurare da muke ganin akwai ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, domin suna kira ga jama’a da su ba su hadin-kai, su zauna lafiya.”
“Duk Juma’a, suna zuwa su yi wa’azi, su na kira ga mutane ka da su kai ‘ya ‘yansu makaranta.”
“Mun kuma ga yadda ‘yan ta’addan suke lafta haraji a kan al’umma domin su iya shiga gonakinsu.”
“Da gangan suke yin wannan domin sun san lokacin girbi ya yi, saboda haka manoma za su yi Allah-Allah su girbi amfanin gonarsu.” - Ahmed Ibrahim Matane

Read also

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Neja na fama da karancin jami'an tsaro

Ahmed Ibrahim Matane yace a yankin Borgu da ke kan iyaka da kasar Benin, ana zargin akwai ‘Yan ISWAP. Matane yace ‘yan sanda 8, 000 rak suke jihar Neja.

Haka zalika lamarin ya ratsa kananan hukumomi irinsu Munya, Shiroro, Rafi, Mariga, da kuma irinsu Msshegu da Lapai da suka yi iyaka da wasu jihohin kasar.

Ayi wa Nnmadi Kanu afruwa?

An yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ca a yankin Arewacin kasar nan a kan yunkurin zagaye kotu, a yafewa shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Kakakin kungyar dattawan Arewa, Emmanuel Yawe ya soki wannan matsaya, yace ta ina za a amince da mutumin da aka ba beli, ya tsere ya cigaba da yin ta'asarsa.

Source: Legit.ng News

Online view pixel