Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai

Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce idan ba a cire tallafin man fetur ba, 35 cikin jihohi 36 baza su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022
  • El-Rufai ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Abuja yayin wani taro na World Bank Nigeria Development Update
  • A cewarsa don gudun haka, a shirye gwamnoni suke da su bayar da hadin kai akan zare tallafin man fetur a wannan lokacin

Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce matsawar ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Abuja a wani taro na World Bank Nigeria Development Update, na watan Nuwamba 2021, inda yace don gudun faruwar hakan, a shirye gwamnoni suke don amincewa da cire tallafin man fetur din.

Read also

Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara idan aka cire tallafi, GMD na NNPC

Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai
Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

A cewarsa, in har ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022.

A cewar El-Rufai, an daidaita kudin kalanzir wanda talakawa suka fi amfani dashi, yayin da aka dade da daidaita kudin Diesel wanda matafiya suke amfani dashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace:

“Batun fetur ne babban abinda ya kamata mu zauna a kasar nan mu tattauna akai kuma mu kawo karshen shi.
“Ba za mu ci gaba da sama wa kasashen da ke makwabtaka da mu fetur ba, don abinda muke ta yi kenan. Me zai sa mu yi hakan? Don wa muke yi? Wanene yake amfana? Mai zai sa muyi hakan yayin da muke tagayyara tattalin arzikin kasar mu?
“Yanzu haka muna tafka asarar N250 biliyan a kowanne wata kuma dole mu dakatar da hakan. Gwamnonin jiha a shirye muke da mu mara wa gwamnatin tarayya baya akan wannan lamari.”

Read also

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Yace Najeriya tana cikin hatsari idan ta ci gaba da bayar da tallafin man fetur

A cewarsa, ya kamata a samu masu ruwa da tsaki su zauna a tattauna kuma a fahimci hatsarin da ake sa kasar nan ciki matsawar aka ci gaba da bayar da tallafin ba tare da kasa tana amfana ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce cire tallafin ba kasafin jihar da ikon kaddamar da ayyuka ne kadai zai taimaka mawa ba, har talaka sai ya more idan aka cire tallafin.

El-Rufai ya ci gaba da lissafo hatsarorin da ke tare da ci gaba da bayar da tallafin inda yace ya kamata a zauna a tsayar da kudin siyar da man fetur na dindindin.

Source: Legit

Online view pixel