Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

  • Hankulan jama'a mazauna yankin Kubwa da ke Abuja ya matukar tashi bayan an tsinta gawar Liman Abdurrashid Usman wanda ya je yin itace
  • Kamar yadda dan uwan mamacin ya sanar, ya bar gida wurin karfe goma na safe amma bai dawo ba, hakan yasa suka dinga nemansa da dare har safiya
  • Daga bisani sun tsinta gawar Liman a wani kango kusa da gona inda suka ga alamun dukansa aka yi da itace a kansa har rai yayi halinsa

Kubwa, Abuja - A ranar Alhamis hankula sun matukar tashi bayan an tsinta gawar limamin makabartar Kubwa mai suna Malam Abdurrashid Usman a gona inda ya je samo wa iyalinsa itace.

Wani dan uwan mamacin mai suna Adamu Sama'ila, ya ce limamin ya bar gida wurin karfe goma na safe amma bai dawo ba, Daily Trust ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

An tsinci gawawwakin mahauta 2 cikin 3 da aka yi garkuwa da su a garin Ala

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona
Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
Ya ce, "Matarsa ta fita domin ba ta gida a lokacin. Ta fita saide-saide. Ta gane cewa ba ya nan ne wurin karfe shida lokacin da ta dawo ba ta tarar da shi ba. Hakan yasa ta yi magana.
"Mun shiga daji wurin gonar Gado-Nasko daga karfe takwas har zuwa 12 na dare amma ba mu gan shi ba. Mun dai samu kayanshi, amalanken da yayi amfani da ita, gatarinsa da itace.
“Daya daga cikinmu ya garzaya ofishin 'yan sanda da ke kwatas din FCDA inda aka kai rahoto.
“A safiyar jiya, mun sake fita nemansa a wuraren kuma muna dab da hakura ne sai wani ya shawarce mu da mu duba har kangon gine-gine da ke da kusanci da mu.
“Mun samu gawarsa inda muka ga raunika a kansa kamar an dinga buga masa itace. Mun kuma samu ice kusa da gawarsa."

Kara karanta wannan

Matar aure ta daɓa wa mijinta, Abdulateef, wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da kwarto a gidansa

Daily Trust ta ruwaito cewa, an birne mamacin mai mata biyu kamar yadda addinin Islama ya tanadar. Limamin dan asalin garin Warawa ne da ke jihar Kano.

Limamin Abuja: Yadda masu shekaru 17 zuwa 19 suka sace ni tare da azabtar da ni

A wani labari na daban, babban limamin masallacin Ƴangoji da ke ƙaramar hukumar Kwali ta Abuja, ya bayyana uƙuba tare da azabar da ya sha a hannun wadanda suka sace shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Liman Abdullahi Abubakar Gbedako, wanda aka sace tare da ɗan shi, ya kwashe makonni uku a hannun masu garkuwa da mutane kuma an sako shi bayan an biya kuɗin fansa har N5 miliyan.

A yayin bayani game da azabar da ya sha a hannun miyagun a gaban manema labarai, limamin wanda shi ne mataimakin shugaban makarantar GJSS Kwaita, ya ce shi da ƴaƴanshi sun matuƙar shan wahala, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kutsen gidan Odili: Malami da wanda ake zargi sun yi uwar watsi

Asali: Legit.ng

Online view pixel