Tuɓe wa ɗaliba hijabi a bainar jama'a: Farfesa Lawal ya bada haƙuri bayan ƙungiyoyin musulmi sun yi ca a kansa

Tuɓe wa ɗaliba hijabi a bainar jama'a: Farfesa Lawal ya bada haƙuri bayan ƙungiyoyin musulmi sun yi ca a kansa

  • Farfesa Ajibade Lawal na jami'ar fasaha ta LAUTECH a jihar Oyo ya bada hakuri kan tilastawa wata daliba cire hijabi
  • Hakan ya biyo bayan rashin jin dadi da wasu kungiyoyin musulmi suka nuna ta hanyar yin zanga-zanga bayan afkuwar lamarin
  • Mijin dalibar, Prince Badmus Yinusa ya amince da hakurin da aka ba shi kuma ya bukaci sauran al’ummar musulmai su bar komai ya wuce

Jihar Oyo, Ibadan - Bayan tashin tarzoma akan dakatar da hijabi ga daliban fannin jinya na jami’ar fasaha ta LAUTECH, Ogbomoso, jihar Oyo da ke Najeriya, an samu maslaha.

Wakilin Legit.ng na reshen jihar Ibadan, Ridwan Kolawole, ya ruwaito yadda shugaban fannin jinya na jami’ar, Farfesa Ajibade Lawal ya ba dalibai da sauran al’ummar musulmi hakuri.

Tuɓewa ɗaliba hijabi a bainar jama'a: Farfesa Lawal ya bada haƙuri bayan ƙungoyoyin musulmi sun yi ca a kansa
Shugabannin kungiyoyin musulmi a Oyo da Farfesa Ajibade Lawal. Hoto: Nurses Affairs
Source: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Tambayoyin da na baku ni ma ba zan iya amsa su ba: Abin mamaki daga lakcara a Najeriya

Kungiyar musulmai ta jihar Oyo ta kirkiri kwamitin bincike akan lamarin kuma ta samu nasarar yin taro da bangarorin da lamarin ya shafa kuma an samu nasarar kwantar da rigimar.

Tun farkon zaman aka janyo aya daga cikin Qur’ani mai girma wacce ta hori mutane da kwantar da tarzoma da yafiya ga junansu.

Kwamitin ta ruwaito yadda shugabanta, Alhaji Kunle Danni da Sakatarensa, Alhaji Mursiku Siyanbade suka saki wata takarda wacce ta shafi har mijin dalibar da aka tozarta, Prince Badmus Yinusa inda duk aka gayyacesu taro a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamban 2021.

An samu bayanai akan yadda shugaban fannin koyon jinya Farfesa Ajibade Lawal ya kasa samun natsuwa bayan ya fahimci munin abinda ya aikata.

Hakurin da farfesa Lawal ya bayar

Ana tuhumar Farfesa Ajibade Bayo Lawal da tozarta musulunci. Bayan fahimtar munin abinda ya aikata ya nuna nadama karara kuma ya dinga rusa kuka tare da neman yafiya daga dalibar da ya tozarta da gaba daya al’ummar musulmai.

Read also

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

Kwamitin ta ruwaito yadda farfesa Lawal ya ba Surveyor Badmus Yinusa hakuri, mijin dalibar, wanda da farko ya yi ikirarin cire matarsa daga bangaren koyon jinyan.

“Mijin dalibar, Prince Badmus Yinusa ya amince da hakurin da aka ba shi kuma ya bukaci sauran al’ummar musulmai da su amince saboda wata ayar Qur’ani da wani Hadith da aka janyo tun farkon zaman, sannan a wurin sai da hawaye suka kwaranya a idanunsa saboda kauna da tsoron Allah da ya shiga jikinsa.”

Mijin ya amince da janye karar da lauyoyin dalibar, Shukurat Ayanbisi Jamiu suka shigar.

Matsayar kungiyar musulmi akan lamarin

Kungiyar musulmai sun yi kira ga hukumar makarantar LAUTECH da kada ta bari dalibar da wasu makamantanta su ci gaba da fuskantar tozarci da cin mutunci saboda addini a yanzu da kuma nan gaba.

Kungiyar musulman ta bukaci hukumar makarantar LAUTECH da ta rubuta a dokokinta cewa ta amince da sa hijabi da nikabi kuma ba za ta sake bari a ci zarafin wani dalibi mai gemu ba.

Read also

EFCC ta sake gurfanar da dan uwan Saraki da tsohon kwamishinan Kwara

An tada hayaniya bayan wani farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a

Tun a baya, kun jicewa akwai yiwuwar rikici ya barke a Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, LAUTECH, da ke Ogbomoso, a ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba idan ba a dauki matakan dakile rikicin ba.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya bayyana cewa wasu kungiyoyin musulmi sun yi zanga-zanga kan abin da suka kira wuce gona da iri da Shugaban tsangayar Koyon Aikin Malaman Jinya, Farfesa Ajibade Lawal ya yi inda ya umurci wata daliba musulmi ta cire hijabi a bainar jama'a.

Source: Legit

Online view pixel