An shirya tsaf, saura kiris a kawo Sunday Igboho Najeriya don ya fuskanci hukunci

An shirya tsaf, saura kiris a kawo Sunday Igboho Najeriya don ya fuskanci hukunci

  • Wani jami'in DSS ya bayyana cewa, a halin yanzu ana kokarin shigo da Sunday Igboho kasar nan don fuskantar hukunci
  • A baya an kame Sunday Igboho ne a jamhuriyar Benin yayin da yake kokarin tsallakewa kasar Turai
  • Ana zargin Sunday Igboho da laifin cin amanar kasa da kokarin dagula zaman lafiya da hadin kan Najeriya

Ibadan - A halin yanzu dai ana ci gaba da shirin shigo da wani dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho zuwa Najeriya, kamar yadda jaridar Punch ta gano.

A baya rahotanni sun bayyana cewa Igboho bayan wani samame da jami’an DSS suka kai gidansa a gidansa na Ibadan don kame shi ya tsere zuwa Cotonou a Jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

Hakazalika rahotanni sun bayyana yadda dubunsa ya cika bayan kama shi da jami’an ‘yan sanda na Brigade suka yi a ranar 19 ga Yuli, 2021, a Cotonou, Jamhuriyar Benin.

Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa | Hoto: thecable.ng
An shirya tsaf, saura kiris a kawo Sunday Igboho Najeriya don ya fuskanci hukunci
Asali: Twitter

Lauyansa, Cif Yomi Aliyu, SAN, ya shigar da karar DSS a madadin Igboho a babbar kotun da ke Ibadan. Daga nan ne kotun ta umarci hukumar DSS da ta biya Igboho zunzurutun kudi har naira biliyan 20 a matsayin diyya, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Sai dai a jerin wasu takardu tare da sanya wa hannun wani jami'in DSS Johnson Oluwole, da ya gabatar a gaban babbar kotun da ke Ibadan a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba, 2021, DSS ta bayyana cewa ana ci gaba da tsare shi domin dawo da shi Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Wani bangaren takardar ya bayyana cewa:

“Gaskiya ne. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ayyana Cif Sunday Igboho a matsayin wanda take nema kuma buya a wasu lokuta a cikin watan Yuni 2021.
“Wannan sanannen lamari ne cewa an kama shi a ranar 19 ga watan Yuli 2021 kuma a halin yanzu yana hannun jami’an tsaron kasar Benin da ke kan kokarin dawo da shi Najeriya.
“Gaskiya ne jami’an tsaro na binciken wanda yake kara kan aikata laifin cin amanar kasa wanda ya saba alakar hadin kan kasa.

Hakazalika, takardar ta bayyana cewa, ya kamata ta duba laifin Igboho, sannan ta yi watsi da batunsa tukuna har sai gwamnatin Najeriya ta gama dashi.

Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

A baya kunji cewa, kotun Jamhuriyar Benin da ke zamanta a Kwatano ta tura Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho zuwa gidan yari, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

An kammala zaman kotun ne misalin ƙarfe 11.20 na daren ranar Litinin bayan shafe kimanin awanni 13.

Wani majiya daga kotun ta shaidawa The Cable cewa ba za a saki Igboho ba. "Matsalar mayar da wanda ake zargin da laifi ƙasarsa domin ya fuskanci sharia lamari ne da akwai siyasa sosai a cikinsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel