An gurfanar da shugaban ƙaramar hukuma kan karɓar cin hanci na miliyoyi daga hannun ɗan kwangila a Abuja

An gurfanar da shugaban ƙaramar hukuma kan karɓar cin hanci na miliyoyi daga hannun ɗan kwangila a Abuja

  • Hukumar ICPC ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Gwagwalada Adamu Danze a gaban kotu
  • An yi karar Danze ne a gaban kotun kan zarginsa da karbar cin hancin Naira miliyan 10 daga hannun wani dan kwangila
  • Mr Danze ya musanta zargin da ake masa, sannan kotun ta bada belinsa kan Naira miliyan 20 ta daga cigaba da shari'ar zuwa Maris din 2022

FCT, Abuja - An gurfanar da shugaban karamar hukuma a birnin tarayya Abuja kan zarginsa da karbar cin hanci daga hannun wani dan kwagila, NewsWireNGR ta ruwaito.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ta gurfanar da ciyaman din karamar hukumar Gwagwalada, Adamu Danze, kan zarginsa da karbar N10m daga hannun dan kwangilar da ke aikin gine-gine a yankin.

Kara karanta wannan

EFCC ta sake gurfanar da dan uwan Saraki da tsohon kwamishinan Kwara

An gurfanar da Mr Danze gaban Mai sharia U.P. Kekemeke na kotun tarayya ta 4 da ke Abuja kan zargin cin hanci da rashawa da amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba.

Abuja: An gurfanar da shugaban ƙaramar hukuma kan karɓar cin hanci na N10m daga hannun ɗan kwangila
An gurfanar da shugaban ƙaramar hukuma a Abuja kan karɓar cin hanci na N10m daga hannun ɗan kwangila. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karar da ta shigar a kotun, ICPC ta zargi Danze da karbar N10m daga hannun shugaban Remotosh Construction Ltd, Engr Aremu Omotosho domin a bashi kwangilar gina tagwayen kwalbati a Paiko-Kore.

A cewar karar da aka shigar, an aikata laifin ne a watan Maris din 2018 inda Mr Danze ya umurci dan kwangilar ya tura wa lauyansa kudin wanda ya saba sassa da dama na dokokin da suka shafi rashawa da cin hanci.

Martanin Mr Danze

Mr Danze, wanda aka riga aka bawa sammaci ya musanta aikata laifukan da aka karanto masa.

Abdul Mohammed, lauyan Danze, ya kuma bukaci kotun ta bada belin wanda ya ke karewa.

Kara karanta wannan

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

Michael Adesola, lauyan ICPC bai goyi bayan bada belin ba.

Alkalin kotun, Mai sharia Kekemeke bayan sauraron bangarorin biyu ya ce wanda ake zargin ba zai tsere ba idan an bada belinsa duba da matsayinsa a gari.

Ya ce:

"Wanda ake zargin shine ciyaman din karamar hukumar Gwagwalada na yanzu don haka ba zai gudu ba. Ba inda zai boye. Don haka za a bada belinsa."

Kotun ta bada belinsa kan kudi N20m tare da wanda zai tsaya masa. Wanda zai tsaya masa ya kasance ya mallaki fili a Abuja ko kuma ma'aikacin gwamnati mai matsayin mataimakin direkta ko sama da haka.

An dage cigaba da sauraron shariar zuwa ranar 1 ga watan Maris na 2022.

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

A wani rahoton, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Kara karanta wannan

Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel