Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

  • Wata mota makare da barasa iri daban-daban ta fadi a kusa da ofishin hukumar Hisbah na Panshekara a Kano
  • Jami'an Hisbah na unguwar sun iso inda abin ya faru sun tattara kwallabe da kiret sannan sun kwace motar giyan
  • Wasu mutanen unguwar da abin ya faru a gabansu sun kaurace wa bada agaji ga motar da ta yi hadari don gujin fushin Allah

Jihar Kano - Wata mota kirar Hilux da ke dauke da barasa ta fada cikin kwata da ke daf da ofishin Hisbah a Panshekara, karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

An rahoto cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata 16 ga watan Nuwamba kuma direban motar ya jikkata.

Mazauna yankin sun garzaya domin kai wa mutanen da ke cikin motar dauki ne sannan suka gano ashe giya ne makare cikin motar.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisba, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah
Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah a Kano, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah
Motar giya da ta fadi a kusa da ofishin Hisbah na Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah
Motar giya da ta yi hatsari a kusa da ofishin Hisbah a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah
Kwallaben giya da suka fashe yayi da motar giya ta yi hatsari daf da ofishin Hisbah a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Da ya ke tabbatarwa Daily Trust lamarin, kakakin Hisbah a Kano, Ibrahim Lawan Fagge ya ce jami'ansu sun tattara kwallaben da suka fashe da sauran kiret din na barasa.

Kakakin na Hisab ya ce:

"Jami'an mu na karamar hukumar sun dade suna fakon motar, sai gashi a ranar ya yi hatsari daf da ofishinmu."

Ya kara da cewa:

"Binciken da muka yi ya nuna cewa direban ya dade yana amfani da Hilux din yana basaja a matsayin motar jami'an tsaro domin jigilar barasa. A yanzu, mun kwace motar, mun ajiye sauran kwalaben a ofishinmu da ke Sharada."

Wasu mazauna Panshekara sun kauracewa motar

Wasu daga cikin wadanda abin ya faru a gabansu kuma mazauna Panshekara dab da ofishin Hisbah a karamar hukumar Kumbotso, sun kaurace wa bayar da agaji ga motar da ta yi hatsari.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

Sun yi hakan ne domin gudun kada tsinuwar Allah ya fada a kansu domin taimakawa wadanda ke jigilar giya wanda haramun ne a musulunci kamar yadda Dala FM ta ruwaito.

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

A wani rahoton mai kama da wannan, Hukumar Hisbah reshen jihar Jigawa ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel