Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu

Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu

  • An tuhumci Zohreh Koudaei, yar kwallon kasar Iran da kasancewa Namiji ce ba mace ba bisa wasu dalilai
  • Dalilin farko shine ta buge fenariti biyu a wasan da Iran ya lallasa kasar Urdu 4-2 a gasar sharen faggen kofin Asiya
  • Gwamnatin Urdu ta yi kira ga gudanar da bincike kan wannan lamari amma gwamnatin Iran ta karyata su

An tuhumci mai tsaron gidan kungiyar kwallon matan kasar Iran, Zohreh Koudaei, da kasancewa namiji bayan nasarar da Iran ta samu kan Jordan a wasar kwallo a Satumba, Sport Bible ta ruwaito.

A cewar hukumar kwallon nahiyar Asiya AFC, Zohreh Koudaei ta buge fenariti biyu a wasan kuma hakan ya jefa shakku cikin abokan hamayyar Iran.

Hukumar ta kaddamar da bincike kan Zohreh Koudaei domin tabbatar da mace ce ko kuma namiji.

Read also

Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai

Ana zargin Golan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu
Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu Hoto: Talibjan Kosimov/Anadolu Agency
Source: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasar Jordan ce ta fara kai kara

Zarge-zargen ya biyo bayan karar da Shugaban hukumar kwallon Jordan, Prince Ali Bin Al-Hussein, ya shigar na neman bincike kan yar wasan.

Mutane sun ce kasar Jordan ta kai kara ne kawai don sun sha kashi a wasar.

Iran ta yi martani

Martani kan hakan, hukumar kwallon Iran ta saki jawabin ta bakin mai zaben yan kwallo, Maryam Irandoost inda ta bayyanawa Varzesh3 cewa:

"Likitocinmu sun duba dukkan yan wasan sosai gudun irin wannan abu, saboda haka jama'a su kwantar da hankulansu."

"zamu gabatar da dukkan bayanan da hukumar kwallon Asiya ke bukata ba tare da bata lokaci ba"

"Wadannan tuhume-tuhumen da ake yi kawai don sun sha kashi hannun yan wasan Iran ne."

"Yan kwallon Jordan na ganin su ya kamata su samu nasara...kuma da suka sha kashi.. sai suka fara kame-kame."

Source: Legit Nigeria

Online view pixel