Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi

Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi

  • Mummunar gobara ta tashi a kasuwar Kurmi da ke jihar Kano inda ta lamushe a kalla shaguna 41 kurmus a daren Litinin
  • Kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta sanar, lamarin ya faru ne wurin karfe 2 amma jami'ansu sun gaggauta kai dauki
  • Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce wutar lantarki ce silar gobarar

Kano - A kalla shaguna 41 ne suka kurmushe sakamakon gagarumar gobarar da ta tashi a fitacciyar kasuwar Kurmi ta jihar Knao a ranar Litinin, hukumar kashe gobara ta sanar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kurmi ta na daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da ke garin Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi
Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Iblitala'in wanda ya fara wurin karfe 2 na dare, ya shafi shagunan masu siyar da litattafai a kasuwar.

Kara karanta wannan

Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi yace, "Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Baba Nasidi wurin karfe daya da minti hamsin da takwas na dare kan cewa gobara ta tashi a kasuwar litattafai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan samun bayanin, mun gaggauta aika masu kashe gobara zuwa wurin inda suka isa karfe biyu da minti bakwai domin kashe gobarar," ya kara da cewa.

Abdullahi ya ce shagunan kari guda 37 da aka yi na wucin-gadi tas suka cinye yayin da wasu shaguna hudu suka cinye bayan taimakon masu kashe wutar.

Ya kara da cewa, wutar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki.

Ya shawarci 'yan kasuwan da sauran jama'a da su dinga kashe dukkanin makunnan kayan wutar su tare da kashe duk wani tushen wuta duk lokacin da ba a amfani da su, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

Kano Tumbin Giwa: Ganduje ya dauki masu rawar koroso 45 aikin dindindin

A wani labari na daban, a ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta mika takardun daukar aikin dindindin ga masu rawar gargajiya wadanda aka fi sani da 'yan rawan koroso 45 a jihar.

Sabbin ma'aikatan rawan da aka dauka aiki an saka su a matsayin kananan ma'aikata ne wadanda za su yi aiki karkashin ma'aikatar tarihi da ofishin al'adu na jihar.

A yayin mika takardun daukar aikin a ma'aikatar, kwamishinan ma'aikatar al'adu, Ibrahim Ahmad Karaye, ya yi bayanin cewa wannan kyautatawar an yi ta ne domin karrama kananan ma'aikata masu aiki tukuru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel