Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i

Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i

Shugabannin kasuwar Oyingbo da ke Legas sun bayar da karin bayani kan dalilin da yasa aka rufe kasuwar na tsawon makonni biyu ta bakin shugaban 'yan kasuwar, Folashade Tinubu-Ojo.

Premium Times ta ruwaito cewa, kasuwar Oyingbo fitacciyar kasuwa ce da ake siyar da kayan abinci a Legas da jihohi masu makwabtaka.

Bayan rufe kasuwar na tsawon makonni biyu, 'yan kasuwar a ranar Laraba sun fito zanga-zanga kan rashin adalcin da aka yi musu.

Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i
Fallasa: Yadda ɗiyar Tinubu ta ƙwace mana kaya, rufe kasuwa kuma ta buƙaci N5m, Jami'i. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sun bayyana dauke da fastoci inda suke rokon Bola Ahmed Tinubu da ya cece su daga diyarsa. A cewarsu, 'ya'yansu na kukan yunwa, ya taimaka ya cece su daga hannun Shade Ojo, diyar Tinubu.

Folashade Tinubu diyar Bola Tinubu ce, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyya mai mulki. An nada ta matsayin shugabar kasuwa mata da maza bayan kakar ta Abibat Mogaji.

Kara karanta wannan

Farashin litan man fetur zai iya tashi N170, Yan kasuwar mai

'Yan kasuwan sun zargi Shade Tinubu da bukatar su tattaro N5 miliyan daga hannunsu ba tare da bada wani notis ba.

Fusatattun 'yan kasuwan da suka bayyana rubabbun abinci a kasa, sun ce rufe kasuwar ya taba kasuwancinsu da kuma hanyar samun kudinsu.

Yadda aka rufe kasuwar

Sakataren kwamitin kasuwar, Lateef Lasisi, ya sanar da Premium Times cewa kusan makonni biyu da suka gabata, Tinubu ta kai ziyara kasuwar kuma ta koka da yadda muhallin ya ke.

"Ta fara korafi bayan ta shiga kasuwar amma mun samu wasika daga karamar hukuma cewa su ne za su kula da tsaftacewa, tsaro da sauransu na kasuwar," yace.
"Amma kuma mu shugabannin, aikin mu kula da tsarin kasuwar a kowacce rana amma ba wai mu kalmashe hannayenmu ba. Hakan mu ke yi a kusan shekaru 2 da suka gabata. Babu abinda muka yi."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

Lasisi ya bayyana cewa, kafin zuwan Tinubu da makonni hudu, gwamnati ta mika tsaro, tsaftacewa da kula da kasuwar hannun kwamitinsu.

"A take tace washegari za ta zo ta rufe kasuwar, a zaton mu wasa ta ke amma tana dawowa ta fara korar jama'a tare da musu watsi da kaya. Hatta bankin da ke cikin kasuwar ta basu minti ashirin kacal," Lasisi yace.

Tara

Lasisi ya ce sun je tare da sauran jami'an kasuwan wurinta a Ikeja amma tace sai sun biya N5 miliyan kafin ta bude kasuwar.

"Wurin karfe 9 na dare na bar wurinta, mu da muka je tun karfe hudu na yammaci," yace.

Ya ce sun je sun hada taro inda suka sanar da 'yan kasuwan cewa an ci su tarar N5 miliyan amma sun bukaci sanin laifin da suka yi. Sun ce karamar hukuma da ke karbar haraji ce ke tsaftace wurin.

Mataimakin shugaban kasauwar, Olateju Muhammed, ya ce Tinubu ba ta bada bayanin dalilin rufe kasuwar ba kafin ta rufe ta.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih a watan Oktoban 2014, ya maka kamfanin sadarwa na MTN a gaban kotu kan cire masa naira hamsin da aka yi kuma aka saka masa wakar kira duk da bai bukata ba.

Kamar yadda shafin @naija_reporter suka ruwaito, bayan fafatawa da aka yi tsakanin Emmanuel na kamfanin MTN, ya samu galaba a shari'ar inda kotu ta umarci MTN da ta biya shi makuden kudi.

A yadda ta kaya a kotun, bayan da alkali ya tabbatar da samun shaidu gamsassu cewa an cutar da shi, an yankewa kamfanin sadarwa na MTN hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: