Malam Isa: Mutumin da ke sayar da aya a baro sanya da kot a Abuja ya bayyana dalilinsa na yin wannan shigar

Malam Isa: Mutumin da ke sayar da aya a baro sanya da kot a Abuja ya bayyana dalilinsa na yin wannan shigar

  • Malam Isa mai Aya dan asalin karamar hukumar Mai Yamma ne da ke jihar Kebbi ya bayyana yadda ya fara sana’arsa a cikin garin Abuja
  • A cewarsa ya ga yadda wani mutum dan garinsu mai sana’a a Abuja ya ke fantamawa kuma kullum yake sauya sutturu iri-iri, hakan ya bashi sha’awar fara sana’a a garin
  • A cewarsa ya fara saka kot ne bayan ya ga yadda ma’aikatan banki da makamantansu su na sa kayan ne suka birge shi, hakan ya sa ya tsiri sakawa

FCT, Abuja - Malam Isa dan asalin jihar Kebbi wanda ya yi fice saboda sanya kot yayin da ya ke tura baro yana sayar da aya ya yi bayanin yadda ya fara sana’ar a hirar da BBC Hausa ta yi dashi.

Read also

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Isa dan asalin karamar hukumar Mai Yamma da ke karkashin jihar Kebbi ne, kuma ya fara sana’ar ne ta dalilin wani mutum dan garinsu kamar yadda ya bayyana a hirar.

Malam Isa: Mutumin da ke sayar da aya a baro sanya da kot a Abuja ya bayyana dalilinsa na yin wannan shigar
Mutumin da ke sayar da aya a baro sanya da kot a Abuja ya bayyana dalilinsa na yin wannan shigar. Hoto: BBC Hausa
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa ya ga mutumin yana sauya sutturu masu kyau hakan yasa ya bukaci binshi daga nan ya fara sana’ar tuka babur bayan an hana a garin sai ya koma sayar da rake, sai yalo sannan aya.

Ya ce yana samun kudi don hidimominsa

Kamar yadda ya ce:

“Alhamdulillahi ina samu, don bakin gwargwado ina samu. Idan na fita ina samu in ci, in sha, in taimaka wa wani kuma har in biya wa yarana kudin makaranta. Kuma har wasu bayin Allah da su ka ga ban sa wa kaina girman kai ba su taimaka min.”

Read also

Dan Najeriya a waje: Yadda dan Najeriya ya hargitsa zaman lafiyar kantin sayayya a kan kudi

A cewarsa ya fara daukar aya a bashi, idan ya siyar ya fitar da riba sai ya mayar a kara ba shi wata har Allah ya ba shi nashi jarin.

Ya ce dalilin da yasa ya fara sa kot idan zai fita don sana’arsa saboda yanda ya ga ma’aikatan banki da sauran makamantansu suna sa wa.

Hakan ya sa ya yi sha’awar fitar da kudi ya siyo. Kuma babban burinsa shine yadda bai samu ya yi karatu ba yaransa su samu suyi.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Read also

Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel