Dan Najeriya a waje: Yadda dan Najeriya ya hargitsa zaman lafiyar kantin sayayya a kan kudi

Dan Najeriya a waje: Yadda dan Najeriya ya hargitsa zaman lafiyar kantin sayayya a kan kudi

  • Wani dan Najeriya mai suna Olalekan, wanda ya yi ikirarin cewa shi “jakada ne” a waje ya haifar da hargitsi a wani babban kanti a kasar Birtaniya
  • Bayan da aka kira masa dan sanda saboda dagula lamari, mutumin ya ce yana son a mayar masa da kudin kayan da ya riga ya siya
  • Yayin da dan sandan ya yi kokarin kwantar masa da hankali, dan Najeriyan ya nuna bacin ransa, yana mai cewa an yi masa ba daidai ba

Wani ‘jakada’ na Najeriya ya yi fito-na-fito da wani dan sanda a kasar Birtaniya. A cikin jerin faifan bidiyo da aka yada a yanar gizo, mutumin ya ce yana son a mayar masa da kudinsa bayan sayen kaya.

Ya bayyana cewa tun da farko an bata masa suna inda aka kira shi da barawo aka kama shi. Lokacin da dan sanda ya kira shi ya tambaye shi ko yana son a mayar masa da kudinsa ne dalilin da ya sa yake ihu a babban kanti, sai ya ce eh.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta

Dan Najeriya a Turai: Yadda matashi ya hargiza zaman lafiyar shagon sayayya kin mayar masa da kudinsa
Yayin da dan sanda ke tambayarsa | Hoto: @instablog9ja
Asali: UGC

Hankalin mutumin daya kuwa?

Mutumin ya ci gaba da cewa dole ne ya daga muryarsa saboda ba a saurare shi ba lokacin da ya bukaci a mayar masa da kudinsa.

Da aka tambayi sunansa, mutumin ya ce shi sunansa Ambasada Olalekan kuma wakilin Yesu almasihu ne.

Ya kara da cewa yana daukar bidyon mutumin a matsayin wani bangare na babban shirin Yesu na tozarta su.

‘Yan Najeriya da dama da suka yi tsokaci a kan faifan bidiyon sun ce maganganun mutumin abun dariya ne.

Kalli bidiyon:

A lokacin rubuta wannan rahoto, faifan bidiyon ya tattara maganganu sama da 3,000 tare da dubban martani.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin kamar haka:

real_kingtee ya ce:

"Muryar da sautin mai daukar bidiyon su kadai abin dariya ne."

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

grt_khali yace:

"Ni da kaina a matsayina na dan Najeriya yana da wuya in fahimci abin da mutumin yake fada. Ambasada yana magana kamar ya bugu."

Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN

A wani labarin, watakila ya gaji da hidimar su, wani dan Najeriya ya kutsa kai bankinsa domin ya bayyana ra’ayinsa na yanke hulda da su.

Mutumin da ya fusata ya hargitsa lamurra yayin da ya yi ihu da babbar murya cewa a rufe asusunsa.

A cikin wani dan gajeren bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, ana iya jin mutumin yana gunaguni game da batun BVN kuma ya fusata da kururuwa tare da cewa 'aikin banza'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel