Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayin da ya cika shekaru 64

Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayin da ya cika shekaru 64

  • A ranar 20 ga watan Nuwamba ne tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi murnar cika shekaru 64 da haihuwa
  • A cikin wani faifan bidiyo mai yawo a kafafen sada zumunta an ga matarsa na rera waka ga mijinta a cikin murya mai ban dariya
  • Bata tsaya nan ba, uwargidan tsohon shugaban kasar ta bayyana Goodluck a matsayin mijinta mai kaunarta yayin da suke murnar bikin

A ranar 20 ga watan Nuwamba ne tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 64, kuma abokai da masu fada aji sun hallara domin bikin tare da shi.

Domin murnar cikar dan siyasar shekaru 64, matarsa, Patience Jonathan, ita ma ta tabbatar da cewa ta nishadantar da shi da wata waka mai ban dariya.

Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayinda ya cika shekaru 64
Jonathan da Matarsa | Hoto: @lindaikejisblog
Asali: Instagram

Yayin da ma'auratan ke cikin wani jirgin sama mai zaman kansa, Patience tare da wasu dangi sun rera wa Goodluck Jonathan wakar zagayowar ranar haihuwa. Duk da haka, muryar matar tsohon shugaban kasar ta fito fili fiye da na kowa yayin da take rera wakar.

A wani lokaci a yayin bikin, Patience ta kuma yi tsokaci kan Goodluck Jonathan yayin da ta bayyana mijin nata a matsayin abin kaunarta a bainar mutanen da ke cikin jirgin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga baya an ga Jonathan yana yanka wani babban kek da ke gabansa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Mutane da dama sun yi martani kan wannan murna da kuma wakar Patience.

Ga kadan daga ciki:

Zayxon_tech:

“Wa kuma ke kewar Patience Jonathan? Ina tunanin ta ba mu dariya duka."

Alfama__8:

“Mama Patience ba za ta taba canzawa ba, ganin tana rera waka kamar yadda ta saba. Muna kewarta Happy birthday sir."

Holla_glamour:

"Ban taba ganin hoton Jonathan ba tare da Patience ba, ALLAH ya kare su da nisan kwana."

Shugaba Buhari ya yabi Jonathan, ya ce kamarsa daban ne a kasar nan

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 da haihuwa wanda ke zuwa a ranar 17 ga Nuwamba, 2021.

Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya taya shi murnar yi wa kasa hidima, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuradiyya a nahiyar Afirka.

A cewar wani yankin sanarwar: "A madadin gwamnati da 'yan Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika gaisawa da tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan da murnar cika shekaru 64 da haihuwa, 17 ga watan Nuwamba, 2021."

Asali: Legit.ng

Online view pixel