Auren su zamu yi, Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da yan mata sama da 20 a Neja

Auren su zamu yi, Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da yan mata sama da 20 a Neja

  • Wasu yan ta'adda da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne sun sace yan mata 22 a wani kauyen jihar Neja
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shaida wa mutanen kauyen cewa ba zasu cutar da su ba, aurensu za su yi
  • Tun a bayan dai kuma a lokuta da dama, Gwamnan Neja ya yi korafin cewa mayakan Boko Haram sun fara kafa sansani a jihar

Niger - Wasu yan ta'adda da ake zaton mayakan Boko Haram ne, sun kai hari kauyen Kurebe dake karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Tribune Online ta rahoto cewa maharan sun yi awon gaba da yan mata 22 yayin famakin, wanda ya auku ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa yan matan da maharan suka sace suna tsakanin shekara 15 da 17 kuma sun shaida wa mutanen ƙauyen auren su zasu yi.

Read also

Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata

Jihar Neja
Auren su zamu yi, Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da yan mata sama da 20 a Neja Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Ya mutane suka ji da lamarin?

Ɗaya daga cikin shugabannin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace yan ta'addan sun umarci a cire matan daga makaranta saboda zasu aure su.

Ya kara da cewa sun yi mamaki da maharan suka zo ranar Alhamis suka ɗauki yan matan, ba tare da jami'an tsaro sun kawo ɗauki ba.

Kazalika ya bayyana cewa shugaban tawagar yan ta'addan, Malam Sadiku, shine yake jagorancin kai hari yankin, kuma yana wa'azi kan tsattsauran ra'ayin musulunci.

Yace:

"Suna cin karen su babu babbaka a yankin, amma da zaran sun ga wata bakuwar fuska, to ko dai su sace shi ko kuma su kore shi daga yankin. Mun kai kukan mu ga hukumomi lokuta da dama."

Dagaske mayakan Boko Haram ne?

A kwanakin baya, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi korafin cewa wasu tawagar yan ta'adda dake da alaka da Boko Haram sun fara kafa tutarsu a Kaure, wanda ke kusa da Kurebe.

Read also

Gwarazan yan sanda sun fatattaki tsagerun yan bindiga, sun ceto mutane da dabbobi a jihar Katsina

Kazalika shugaban karamar hukumar Shiroro, Kwamaret Suleiman Dauda Chukuba, ya yi korafi kan ayyukan wannan tawaga, kuma ya nemi a ɗauki mataki.

A wani labarin na daban kuma wani Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi, yace gwamnatin Najeriya zata iya kawo karshen matsalar tsaro idan ta so.

A cewarsa matukar gwamnati zata iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wurraren da lamarin ya yi kamari, to komai mai sauki ne.

Source: Legit.ng

Online view pixel