Jirgin yakin sojoji ya yi ruwan bama-bamai kan sansanonin yan bindiga a Arewa, ya hallaka manya-manyan su

Jirgin yakin sojoji ya yi ruwan bama-bamai kan sansanonin yan bindiga a Arewa, ya hallaka manya-manyan su

  • Jirgin yakin rundunar sojin sama ya aiwatar da hare-haren bama-bamai ta sama kan sansanonin yan bindiga a Arewa
  • Rahoto ya bayyana cewa manyan kusoshin yan bindiga da shugabannin su, sun mutu yayin harin a Sokoto, Zamfara
  • A cewar wani jami'in soji, sabbin dabarun da dakarun sojin kasar nan suka fara amfani da shi ya fara haifar da ɗa mai ido

Sokoto - Wani ruwan bama-bamai da jirgin yakin rundunar Operation Hadarin Daji ya yi, ya hallaka adadi mai yawa na yan bindiga a yankin arewa ta yamma.

A rahoton PRNigeria, harin jirgin yakin, wanda sojojin sama suka aiwatar a Dangwandi da Tsakai dake karamar hukumar Isa, ya yi sanadin mutuwar ƙusoshin yan bindiga da dama.

Kazalika makamancin irin wannan ruwan bama-baman ta sama, ya hallaka kayayyakin amfani yan bindiga da yawan gaske a wasu sassan Zamfara.

Read also

Abu daya ya rage mu kawo karshen yan ta'adda da yan bindiga a Najeriya, Hafsan Soji

Jirgin yakin sojoji
Jirgin yakin sojoji ya yi ruwan bama-bamai kan sansanonin yan bindiga a Arewa, ya hallaka manya-manyan su Hoto: leadership.ng
Source: UGC

Mutum nawa sojojin suka kashe?

Wata majiya a yankin da lamarin ya shafa, ya bayyana cewa sun ga tulin gawarwakin yan bindiga a sansanonin su daban-daban.

Hakanan kuma harin sojin ta sama ya lalata kayayyakin su da tatattalin arzikin da suke da shi, inji majiyan.

A cewar majiyan, Dakarun sojin ƙasa sun bude wa yan bindigan da suka yi kokarin tserewa daga harin saman, sun hallaka su.

Leadership ta rahoto majiya daga cikin jami'an tsaron sirri tace:

"A takaice sansanin kasurgumin ɗan Bindiga, Bello Guda Turji, da kuma yaron sa, kwamanda Bello Buzu, tare da mabiyansu, na daga cikin wuraren da sojojin suka saki wuta ta sama da kasa."
"Nasarorin da aka samu musamman ta harin jirgin yakin NAF a yankin arewa ta yamma da arewa maso gabas ya tabbatar da cewa sabbin dabarun da hukumomin soji suka ɗauka ya fara haifar da sakamako mai kyau."

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

A wani labarin kuma Mayakan Boko Haram sun sace yan mata 22 a jihar Neja, sun bayyana cewa auren su zasu yi

Wasu yan ta'adda da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne sun sace yan mata 22 a wani kauyen jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shaida wa mutanen kauyen cewa ba zasu cutar da su ba, aurensu za su yi.

Source: Legit

Online view pixel