Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce

Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wata budurwa da ta yi karin gashi da ke jan kasa.
  • An tattaro cewa matashiyar ta kashe naira dubu 657 don yin karin gashin mai tsawon inci 150.
  • Mutane da dama sun soki hakan, inda wasu ke mata kallon mai cike da wauta da sunan kwalliya.

Kamar yadda kuka sani idan aka zo kan maganar ado da kwalliya, wasu matan kan yi duk mai yiwuwa don ganin sun kece raini tare da fita daban a cikin sa’anninsu.

Kama daga abun da ya shafi takalma, tufafin sanyawa, gyaran gashi da sauransu, kowa na da irin nasa salon birgewar.

Hakan ce ta kasance ga wata budurwa wacce ta yi fice a yanar gizo da shafukan soshiyal midiya saboda irin salon nata gyaran gashin, inda ta yi karin gashi wanda ke da tsawo har yana jan kasa.

Kara karanta wannan

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba

Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce
Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce Hoto: @nigerianbraids
Asali: Instagram

A wani bidiyo da shafin @nigerianbraids ya sanya a Instagram an gano wata matashiyar budurwa tana baza karin gashi da tayi wanda ke dauke da launin ja, ya kai har kitson nata na jan kasa saboda tsabar tsawonsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon, an gano matashiyar na tattara karin gashin nata mai tsawon inci 150 kuma a bisa ga rubutun da ke kasan bidiyon, tsadar gashin ya kai naira dubu 657 ($1600).

Kalli bidiyon a kasa:

Tuni bidiyon ya janyo cece-kuce daga mabiya shafin

Legit Hausa ta tattaro maku wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi a kan kitson matashiyar.

mide_esther ta ce:

"Da wani zai take daya daga cikin wadannan kitso..ciwon kai na gaske kenan."

tracy_ani ta yi martani:

"Yanzu ana kwana biyu za ta kwance shi."

oma_sintia:

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

"Ka dubi irin gwagwarmayar da ta sha don kawai za ta dauki hoto."

oluwaferintomi:

"Wahala na zaman-zamansa, kin je kin dauke shi a kai."

shantelsucre_1:

"Shirme kawai."

queintessence:

"Wani irin hauka ne wannan."

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

A wani labari na daban, wasu matasan 'yan Najeriya sun nuna wa duniya cewa ana iya damawa da su a kowani yanayi, kuma a shirye suke su shiga a fafata da su a duniyar kera motoci.

Duk da tarin kalubale da suka fuskanta ta fuskacin kudi, kayan aiki da tallafi daga hukumomi, matasan sun kera motocin da ya ja hankalin mutane da yawa.

A wannan zaure, Legit.ng za ta waiwayi wasu matasan yan Najeriya uku da suka nunawa duniya hazikancinsu a bangaren kere-kere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel