Da duminsa: Kotu ta garkame dalibin jami'a da ya yiwa Lakcara dukan kawo wuka

Da duminsa: Kotu ta garkame dalibin jami'a da ya yiwa Lakcara dukan kawo wuka

  • Matashin da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka ya gurfana gaban kotun majistare a jihar Kwara
  • Waliyullah Salaudeen ya bayyana dalilin da ya sa ya lakadawa Malamarsa duka cikin ofishinta
  • Lauyansa ya bukaci Alkali ya bashi beli amma Lauyan yan sanda ya bukaci a garkameshi a kurkuku

Ilorin - Dalibin ajin karshe da aka kora daga jami'ar Ilori, Waliyullah Salaudeen, kan yiwa Malamarsa Dr Rahmat Zakariya, dukan tsiya ya sha garkama bisa umurnin kotu.

Daily Trust ta ruwaito cewa kotun Majistare ta baiwa yan sanda umurnin garkame Waliyullah ne ranar Juma'a a zaman da akayi a Ilori.

A cewar sanarwar yan sanda, Matashin ya debi kwayoyi kafin shiga ofishin Malamar.

Takardar cajin yan sanda yace:

"Ance yana shiga ya fara bugun teburinta, ya fara mata iwun ta bashi maki a aikin SIWES alhalin bai yi aikin ba."

Read also

Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA

"Sai ya nausheta lokacin da taki kuma yayi mata dukan kawo wuka. Abin ya kai ga sai da ya fasa gilashin tagar ofishin da niyyar caka mata kwalba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Malamar ta kama iwu har jama'a suka jita suka kawo mata dauki."

Da duminsa: Kotu ta garkame dalibin jami'a da ya yiwa Lakcara dukan kawo wuka
Da duminsa: Kotu ta garkame dalibin jami'a da ya yiwa Lakcara dukan kawo wuka
Source: UGC

Lauyan Yan sanda, Insfecta Nasr Yusuf, ya bukaci kotu ta garkame shi.

Amma lauyansa, A.B Bakare, ya bukaci a baiwa dalibin beli.

Alkali Muhammad Ibrahim ya bayyana umurnin garkame Waliu kuma ya dage zaman zuwa ranar 26 ga Nuwamba, 2021.

Matashin da ya lakadawa lakcararsa dukan bayyana dalilin yin hakan

Waliyullah Salaudeen, ya bayyana dalilin da ya sa ya lakada wa wata lakcararsa, Mrs Zakariyau dukan kawo wuka.

A cewar dalibin wanda aka fi sani da Captain Walz, ya yi hakan ne sakamakon kin taimakonsa da lakcarar ta yi na wajen karkata tsarin SIWES da take duba shi akai.

Read also

‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli

Walz ya zanta da tawagar ‘yan jaridu a harabar Jami’ar, wadanda suka gana da shi a ofishin jami’an tsaron jami'ar bayan kama shi jim kadan bayan faruwar lamarin.

Dalibin ya yi ikirarin cewa watanni kafin faruwar lamarin a ranar Alhamis din da ta gabata, an kama shi tare da kulle shi na tsawon watanni biyu a Legas wanda hakan ya sa ya kasa zuwa yin shirin na SIWES.

Source: Legit.ng

Online view pixel