‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli

‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli

  • Sanata Ibrahim Shekarau ya zolaye Gwamna Ganduje na jihar Kano a kaikaice yayin da ya ke yi wa magobaya bayansa jawabi a Kano
  • Shekarau, yayin jawabinsa ya jefa tambaya ga al'umma yana mai cewa 'wanene sarkin cusa daloli' a aljihunsa
  • Hakan na zuwa ne bayan cikin 'yan kwanakin nan Ganduje ya soki Shekarau inda ya ce bai tsinanawa mutanen mazabarsa komai ba duk da kudin da ya ke samu a Abuja

Kano - Sanata mai wakiltar Kano Central, Ibrahim Shekarau, ya caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan fitaccen bidiyon dalolli da ke nuna gwamnan yana soke dalolli a aljihunsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Ganduje ne ya fara sukar Shekarau a ranar 14 ga watan Oktoba yayin taron yan siyasa a Africa House, gidan gwamnati, a lokacin da ya zargi Shekarau da Sanata Barau Jibrin da 'karbar kudi a Abuja' ba tare da yi wa mutanensu komai ba.

Read also

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli
‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Dala. Hoto: Daily Nigerian/The Nation
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ka gaza yi wa mutanen mazabunka ayyuka masu kyau kuma da ka fara fuskantar matsaloli, sai ka dora laifin a kai na?
"Kudin da kake karba a Abuja bai isa iso mazabunka ba, yanzu kuma kana neman dora min laifi? Shin ni ne na janyi maka matsalalolin?,' - a cewar Ganduje

Martanin Shekaru

Da ya ke yi wa taron magoya bayansa jawabi a gidansa da ke Mundubawa a Kano a ranar Talata, Shekarau ya yi hannunka mai sanda ga gwamnan a matsayin 'Sarkin Cusa' Daloli.

Sanatan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kira wani fitaccen mai bada gudunmawa a shirye-shiryen gidajen rediyo, Alhaji Nagoda, ya zo ya fada wa mutane ko wanene gwanin soke daloli a aljihunsa.

Nagoda ya yi fice wurin magana kan Ganduje a rediyo game da bidiyon dallolin.

Read also

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

"Alhaji ya yi ikirarin cewa shune shugaban masu karba, amma yanzu ina kiransa ya zo ya fada wa mutanen Kano wanene sarkin cusa daloli," In ji Shekarau, yayin da mutane ke tafa masa.

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

A wani rahoton, rikicin siyasa da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano da Sha'aban Sharada, mai wakiltar Kano Munincipal a Majalisar Tarayya na kara kamari a yayin da Ciyaman din Kano Municipal ya yi jagoranci aka rusa filin da dan majalisar zai yi gini.

A watan Oktoba, an fara sa in sa tsakanin gwamnatin Kano da yan majalisar tarayya hudu a yayin da yan majalisar suka kai kara wurin uwar jam'iyya game da rikicin da ke faruwa a APC a Kano, rahoton Daily Trust.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen soshiyal midiya ya nuna yadda shugaban karamar hukumar Kano Municipal, Fa'izu Alfindiki ya jagoranci matasa sun rushe wurin da dan majalisar zai yi gini.

Read also

Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel