Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara

Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake bude wasu kasuwanni da aka rufe sakamakon ayyukan 'yan bindiga a jihar
  • Kasuwannin sune na dabbobi da ke Gummi, Bagega, Danjibga, Kasuwar Daji, Tsafe, Talata-Mafara da na Nasarawar Godel
  • Mai ba gwamnan shawara a harkokin labarai, Zailani Bappa, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma'a

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sanar da sake bude wasu kasuwanni da aka rufe a baya sakamakon hare-haren 'yan bindiga a jihar, Daily Nigerian ta rahoto.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, daga mai ba gwamnan shawara a harkokin labarai, Zailani Bappa, Matawalle ya yi sanarwar ne a yayin rantsar da kwamishinoni biyu, hadimai 10, sakatarori takwas da babban mai binciken kashe kudaden jihar.

Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara
Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A cewar sanarwar, gwamnan ya yanke shawarar sake bude wasu daga cikin kasuwannin ne sakamakon inganci da aka samu a lamarin tsaro a jihar a watan da ya gabata.

Har ila yau, gwamnan ya bude kasuwannin ne saboda damuwa da mawuyacin halin da rufe kasuwar ya jefa tattalin arzikin jihar a ciki.

Kasuwannin da aka bude sun hada da na dabbobi da ke Gummi, Bagega, Danjibga, Kasuwar Daji, Tsafe, Talata-Mafara da na Nasarawar Godel.

Sai dai kuma, Matawalle ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar za ta hukunta duk mutum ko kungiyoyin da ke kashe mutane a kasuwanni.

Matawalle ya ce:

"Duk wanda aka kama yana karya wannan doka zai fuskanci hukuncin da ya dace. Don haka ina kira ga kungiyoyin ‘yan banga da wadanda abin ya shafa da su bi doka da oda wajen magance duk wata matsala da ka iya tasowa a irin wannan yanayi”.

A ruwayar Punch, gwamnan ya yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran shugabanni da su tabbatar da ganin cewa an sanya idanu sosai a kan sabon matakin, inda ya bayar da tabbacin cewa za a sake sassauta wasu matakan nan gaba kada.

Zamfara: Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC

A wani labarin, jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce ta shigar da kara a kotu na kalubalantar Hukumar tsare birane na Zamfara, ZUREP, saboda shirin rusa sakatariyar ta da ke Gusau.

Bala Mande, shugaban kwamitin riko na jihar, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron shugabannin jam'iyyar a sakatariyar a ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Mande, tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamna Bello Matawalle ya cigaba da zamansa a jam'iyyar PDP bayan gwamnan ya sauya sheka zuwa APC a ranar 27 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel