Da dumi-duminsa: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

Da dumi-duminsa: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

  • Shugabannin kabilar Igbo daga kudu maso gabas sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa
  • Zuwa yanzu ba a san ajandar ganawar da suka yi ba a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba
  • Sai dai ana ganin ba zai rasa nasaba da lamarin tsaro a kudu maso gabas da kuma kamun shugaban awaren IPOB, Nnamdi Kanu ba

Abuja - Manyan shugabanni daga yankin kudu maso gabas sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa, Abuja, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

Mataimakin shugaban kasa a shafukan sadarwar zamani, Buhari Sallau ya sanar da batun ganawar tasu a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Dattijo Hon. Mbazulike Amaechi ne ya jagoranci tawagar wacce ke dauke da tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Chukwuemeka Ezeife.

Kara karanta wannan

Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da Buhari a Aso Rock Villa

Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa
Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Har ila yau a tafiyar akwai mataimakin shugaban kungiyar zaman lafiya na addinai, Bishop Sunday Onuoha, Mista Tagbo Amaechi, da Chief Barr. Goddy Uwazurike.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministan kwadago da daukar ma'aikata, Chris Ngige, ministan kimiya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu, ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama da kuma ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba.

Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya duk sun hallara.

Sai dai ba a bayyana ajandar taron ba domin tawagar basu cewa manema labarai uffan ba bayan ganawar.

Amma kuma ana ganin baya rasa nasaba da yanayin tsaro a kudu maso gabas da kuma kamu da tsare shugaban kungiyar awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

Akwai yiwuwar Gwamnati ta sasanta da Nnamdi Kanu da Igboho a wajen kotu inji Malami

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Villa

A wani labarin, mun ji a baya cewa gwamnatin tarayya tace za ta iya la’akari da duk wata hanya wajen kawo karshen rikicin da masu neman a barka kasar nan suke neman jawowa.

Jaridar This Day ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji Ministan shari’a, Abubakar Malami, yana fadan wannan.

Abubakar Malami (SAN) ya nuna cewa gwamnatin Najeriya za ta iya neman mafitar siyasa a wajen kotu da irinsu Nnamdi Kanu da kuma Sunday Igboho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel