Akwai yiwuwar Gwamnati ta sasanta da Nnamdi Kanu da Igboho a wajen kotu inji Malami

Akwai yiwuwar Gwamnati ta sasanta da Nnamdi Kanu da Igboho a wajen kotu inji Malami

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari tace ba ta rufe kofar sasantawa da masu neman a raba kasa ba.
  • Yanzu haka wasu masu wannan ra’ayi irinsu Nnamdi Kanu da Sunday Igboho suna shari’a a kotu.
  • AGF Abubakar Malami SAN yace Najeriya na iya duba batun sasantawa ba tare da an bi ta kotu ba.

Abuja - Gwamnatin tarayya tace za ta iya la’akari da duk wata hanya wajen kawo karshen rikicin da masu neman a barka kasar nan suke neman jawowa.

Jaridar This Day ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021, inda aka ji Ministan shari’a, Abubakar Malami, yana fadan wannan.

Abubakar Malami (SAN) ya nuna cewa gwamnatin Najeriya za ta iya neman mafitar siyasa a wajen kotu da irinsu Nnamdi Kanu da kuma Sunday Igboho.

Manema labarai sun tambayi babban lauyan gwamnati ko za a iya yin sulhu da Sunday Adeyemo da Mazi Nnamdi Kanu, sai yace ba a rufe kofar yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

Martanin da Abubakar Malami ya bada

“Idan ana maganar sha’anin tsaro da shugabanci, wannan gwamnati ba za tayi watsi da duk wata hanya ba. Amma dai sai an duba tukun.” – Malami.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malami
AGF Malami da Shugaban kasa Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

“Duk da za mu duba wadannan ta fuskar nauyi, inganci da kyakkyawan zato, kuma mu duba abubuwan da suke tasiri wajen yin irin wannan yarjejeniya.”
“Saboda haka ba abu bane da mutum zai dauki mataki ba tare da ya duba abin da zai je ya dawo ba. Sai an yi la'akari da abin da zai iya faruwa ko akasinsa”

Korafin da NGF take yi a kan Malami

Wani rahoto da Punch ta fitar, yace Ministan ya yi magana a kan surutun da gwamnoni suke yi a dalilin kudin da gwamnatin tarayya ta ba masu bincike.

Malami yace an cire wadannan kudi ne a dalilin wata shari’a da aka yi tun a 2013, kuma kungiyar gwamnoni da ALGON duk sun sa hannunsu a maganar.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Ministan yace ya cire wadannan makudan kudi ne domin gudun bashi ya taru a kan gwamnatin tarayya, ba don yana da alaka da wadanda suka yi aikin ba.

Me Gwamnoni suke fada a kan Ministan?

Kwanaki Gwamnatin Muhammadu Buhari ta biya masu bada shawara kudi har Naira Biliyan 170 daga cikin asusun da Gwamnoni 36 suke da hakki a kai.

Wannan ya sa kungiyar NGF take zargin AGF da gaggawar zaftare wadannan kudi bayan kotu ta dakatar da ita, sannan gwamnoni suka ce an sabawa doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel