Kaduna: SUBEB na shirin mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su da sauransu makaranta

Kaduna: SUBEB na shirin mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su da sauransu makaranta

  • Gwamnatin Kaduna na shirin mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su makaranta
  • Hakazalika hukumar SUBEB ta kuma ce za ta mayar da mata 24,000 da yara marasa gata 16,500 makaranta a kananan hukumomi 14 na jihar
  • Shugaban hukumar SUBEB, Alhaji Tijjani Abdullahi, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba bayan wani taron masu ruwa da tsaki

Jihar Kaduna - Hukumar makarantar firamare ta jihar Kaduna ta tattauna da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su makaranta.

Shugaban hukumar SUBEB, Alhaji Tijjani Abdullahi, ya bayyana hakan a wajen taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba.

Kaduna: SUBEB na shirin mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su da sauransu makaranta
Kaduna: SUBEB na shirin mayar da almajirai 10,500 da aka dawo da su da sauransu makaranta Hoto: Punch
Source: UGC

Ya ce za a bayar da kyauta ga jihohin da suka yi nasarar mayar da almajiran da aka dawo da su makaranta.

Read also

Zamfara: Matawalle Na Shirin Rusa Sakatariyar Jam’iyyar PDP Bayan Ya Koma APC

SUBEB tana kuma shirin mayar da mata 24,000 da yara marasa gata 16,500 makaranta a kananan hukumomi 14 na jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto cewa shirin BESDA wani tallafi ne da bankin duniya ta bai wa Najeriya na dalar Amurka miliyan 611 don mayar da yara makaranta.

Masu ruwa da tsakin da za su shige gaba wajen mayar da yaran makaranta su ne; Sakatarorin ilimi, jami’an wayar da kan jama’a, shugabannin zamantakewa da wayar da kan jama’a na kananan hukumomi 14 da sauransu.

Abdullahi wanda ya samu wakilcin daraktan tabbatar da inganci, Malam Tanko Aliyu, ya bayyana cewa kananan hukumomin da aka zaba sune ke da almajirai da yawa.

A cewarsa, gwamnatin jiha za ta mayar da kudaden da aka ware domin shirin mayar da yaran makaranta idan har ba a cimma manufar aikin ba.

Read also

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Ya bukaci wadanda aka mika wa ragamar aikin da su yi aiki tukuru domin cimma nasara saboda ci gaban al’umma da jihar baki daya.

Ya ce:

"Ba mu da lokaci, sai dai, manufar ba shine tukwicin da za a bai wa kowane yaro namiji ko mace da aka mayar makaranta ba, illa don daraja da muhimmancin ilimi ga yaranmu wadanda su ne shugabanninmu na gobe. Da ilimi, za a magance yawancin matsalolin zamantakewa da rashin tsaro, da haka, za mu iya bacci da idanunmu biyu a rufe."

Misis Josephine Rikichi, babbar jami’ar kididdiga ta SUBEB, ta ce an zabi almajirai da aka dawo dasu ne sakamakon kiran da kasar ta yi na a mayar da dukkan almajirai daga jihohin kasar gaban iyayensu.

Rahoton ya kuma ce masu ruwa da tsakin da ke da alhakin isar da wannan aiki, za su wayar da kan iyaye da yaran da aka dawo da su da kuma shugabannin gargajiya a kananan hukumomin.

Read also

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani

A wani labari na daban, gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yace gwamnatinsa zata yi aikin gyaran makarantun Almajirai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ranar Asabar, a wurin rufe taron ƙara wa juna sani kan makarantun almajirai, Tambuwal yace gwamnatinsa zata yi iyakar bakin kokarinta wajen tabbatar da wannan gyara.

Gwamnan yace:

"Ba mu da shirin hana karatun tsangaya na haddar Alkur'ani, domin wasu mutane sun fara rokon Sokoto ta bi sahun sauran jihohi."

Source: Legit.ng

Online view pixel