Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU

Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU

  • Kakakin majalisar wakilan Najeriya ya gana da Ministar kudi da karamin ministan ilimi da ASUU
  • Majalisar wakilan tarayya ce ta bukaci Kakakinta ya sanya baki cikin wannan lamari bayan barazanar ASUU
  • Gwamnatin tarayya tayi yarjejeniya da ASUU tun 2009 amma har yanzu ana kai ruwa rana kan lamarin

Abuja - An cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU da Gwamnatin tarayya kan kudin alawus N22.17 billion da N30 billion kudin gyaran jami'o'i.

An cimma wannan matsaya ne ranar Alhamis yayin zama da Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya shirya na sulhu tsakanin bangarorin biyu, rahoton Premium Times.

Wadanda ke halarce a zaman sun hada da shugaban ASUU, Emmanuel Sodeke; Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed; Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba.

Majalisar a ranar Talata ta yanke shawaran sanya baki cikin wannan lamari sakamakon gabatar da kudirin da Julius Ihonvbere (APC, Edo) yayi.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: Dan majalisa na PDP ya nemi Buhari ya tsige Lai Mohammed

Kaakin Majalisa Gbajabiamila a jawabin bude taron ya caccaki gwamnatin tarayya kan kin cika alkawarinta, kuma yayi kira da ASUU su daina barazana ko yaushe da yajin aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU
Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU Hoto: TVC
Asali: Facebook

A ganawar, Shugaban ASUU yace tun shekarar 2009 suka baiwa gwamnati damar cika alkawuranta amma har yanzu an ki cika musu.

Ya ce yanzu babu wani sulhun da zasu yarda da shi fiye da gwamnati ta biya bilyan 30 cikin bilyan 220 don gyaran jami'o'i da kuma N22.17 billion kudin alawus dinsu.

Farfesa Osodeke yace:

"Mun hadu a Agustan 2021, mun fadawa mambobinmu su kwantar da hankulansu saboda an mana alkawarin cewa a watan za'a biya."

Ya kara da cewa sun yanke shawara daukan mataki ne lokacin da suka ga gwamnati ba tada niyyar cika alkawarinta.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed tace tuni ma'aikatar ilimi tuni ta bada umurnin a biya kudaden, Ta ce nan da mako guda za'a biya duka kudaden.

Kara karanta wannan

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

Ta ce ma'aikatar na sauraron tsarin yadda za'a biya kudin ne daga hukumar kula da jami'o'i NUC, kuma ana bata tsarin za'a tura kudaden makarantun.

Akwai kudi, ba zamu bari ASUU su sake shiga yajin aiki ba, Ministan Buhari ya bugi kirji

A baya, Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, yace barazanar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na sake tsunguma yajin aiki ba zata cika ba.

The Cable ta rahoto cewa ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin mako uku ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma wa a baya.

Da yake jawabi a wurin wata hira da kafar watsa labarai ta Channels TV, Ngige ya tabbatar da cewa an ware kuɗaɗen da za'a tura wa jami'o'in.

Asali: Legit.ng

Online view pixel