Akwai kudi, ba zamu bari ASUU su sake shiga yajin aiki ba, Ministan Buhari ya bugi kirji

Akwai kudi, ba zamu bari ASUU su sake shiga yajin aiki ba, Ministan Buhari ya bugi kirji

  • Gwamnatin tarayya tace ba zata bari kungiyar ASUU ta sake shiga yajin aiki ba duk da barazanar da suka yi
  • Ministan kwadugo, Chris Ngige, ya bayyana cewa tuni ma'aikatar ilimi suka kammala shirin tura kuɗaɗen asusun jami'o'i
  • Sai dai yace bai kamata a bar komai da ya shafi ilimi a hannun gwamnati ba, ita kaɗai ba zata iya ba

Abuja - Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, yace barazanar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na sake tsunguma yajin aiki ba zata cika ba.

The Cable ta rahoto cewa ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin mako uku ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma wa a baya.

Da yake jawabi a wurin wata hira da kafar watsa labarai ta Channesl TV, Ngige ya tabbatar da cewa an ware kuɗaɗen da za'a tura wa jami'o'in.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Chris Ngige
Akwai kudi, ba zamu bari ASUU su sake shiga yajin aiki ba, Ministan Buhari ya bugi kirji Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Ministan yace:

"Ba zamu bari su shiga yajin aiki ba, abinda nasani an ware kuɗin da za'a basu, kuma ma'aikatar ilimi ta bani tabbacin gobe za su fitar da takardu domin tabbatar da kuɗaɗen sun shiga asusun jami'o'i."
"Ba zamu baiwa ƙungiyar kuɗi kai tsaye ba, saboda haka kuɗaɗen za su shiga asusun jami'o'i ne kai tsaye."

Meyasa ake barin bangaren Ilimi yana ja baya?

Ministan ya kara da cewa bangaren ilimi na kara samun koma baya, kuma ba zai yuwu ace gwamnati ce kaɗai zata samar da kuɗaɗe a ɓangaren ba.

"Halin da ilimi ke ciki a yanzun ba abin murna bane, na yarda kullum koma baya ake samu, amma gwamnati ba zata iya ɗauke ragamar bangaren ba baki daya."
"Nasan haka saboda a Najeriya na yi karatu na, na yi Firamare anan, Sakandire anan kuma na wuce jami'a anan Nsukka, Enugu."

Kara karanta wannan

Harin Sokoto: Kada ku yi tunanin banza kuke ci kan yan Najeriya, Shugaba Buhari ya gargaɗi yan bindiga

"Na yi karatun digiri na biyu a kasar waje, amma zan iya tabbatar ma da cewa a can ba gwamnati kaɗai ke ɗaukar nauyin ɓangaren ilimi ba."

A wani labarin kuma Pantami yace Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, yace nan gaba kadan za'ai mamakin matakin da Najeriya zata hau.

A cewarsa tattalin arzikin zamani na Najeriya zai shiga sahun mafi karfi a duniya nan da wasu shekaru kalilan masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel