Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

Barazanar sabon yajin aiki: Kakakin Majalisa ya shiga tsakanin ASUU da Gwamnatin tarayya

  • Kakakin majalisar wakilan Najeriya yana ganawa da wasu manyan jami'an gwamnati da ASUU
  • Ya gana da ministan ilimi da ministar kudi, da shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya wato ASUU

FCT Abuja - Kakakin majalisar wakilan tarayya, Mr Femi Gbajabiamila ya yi zaman sulhu tsakanin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU da Gwamnatin tarayya.

TVC ta ruwaito cewa wannan zama na gudana ne a dakin taron dake cikin majalisar a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2021.

Wadanda ke halarce a zaman sun hada da Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed; Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba, da tawagar ASUU.

Akwai kudi, ba zamu bari ASUU su sake shiga yajin aiki ba, Ministan Buhari ya bugi kirji

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige, yace barazanar kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na sake tsunguma yajin aiki ba zata cika ba.

The Cable ta rahoto cewa ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin mako uku ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma wa a baya.

Da yake jawabi a wurin wata hira da kafar watsa labarai ta Channels TV, Ngige ya tabbatar da cewa an ware kuɗaɗen da za'a tura wa jami'o'in.

Asali: Legit.ng

Online view pixel