Labari mai dadi: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 4.03% inji rahoton NBS

Labari mai dadi: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 4.03% inji rahoton NBS

  • Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi mai dan tsoka tun bayan barkewar annobar Korona a shekarar 2020
  • Tattalin arzikin na Najeriya ya karu da 4.03%, wanda ya zarce na kwata hudu da suka shude a shekarar 2020 da tsakiyar 2021
  • A rahoton da muka tattaro, an bayyana bangarorin da suka jawo kashi mai tsoka ga tattalin arzikin kasar

Abuja - Simon Harry, babban jami'in kididdiga na tarayya, ya ba da sanarwar cewa tattalin arzikin kasar ya karu da 4.03% a kwata na uku na shekarar 2021, TheCable ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wani taron manema labarai kan halin da ake ciki a halin yanzu na arzikin kasa (GDP).

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Harry ya yi bayanin cewa mummunan alkaluman GDP da aka samu a 2020 sakamakon cutar Korona sunyi tasiri kan alkalumman GDP na kwata na biyu da na uku na 2021.

Labari mai dadi: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 4.03% inji rahoton NBS
Tattalin arzikin Najeriya ya karu | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ci gaban da ake gani a karuwar tattalin arzikin da aka samu a kwata na hudu da suka gabata yana nuna ci gaban da aka samu wajen dakile cutar ta Korona da kuma mummunan tasirin da ke tattare da rayuwa, jin dadi da tattalin arziki.

A cewar rahoton na NBS inji NairaMetrics, ainihin GDPn Najeriya ya karu da kashi 4.03 cikin 100 a cikin Q3 2021, wanda ke wakiltar ci gaba a hankali idan aka kwatanta da 5.01% da aka samu a kwatan baya.

A kan kwata-kwata ainihin GDP ya karu da 11.07% a cikin Q3 2021 idan aka kwatanta da Q2 2021, yana nuna babban ayyukan tattalin arziki fiye da kwata na baya.

Kara karanta wannan

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

A halin da ake ciki kuma, bangaren mai ya samar da 10.73% a shekara a daidai wannan lokacin. Samarwar, ya danganta ne da raguwar hako danyen mai.

A cewar NBS, yawan man da ake hakowa a Najeriya ya kai 1.57mpd idan aka kwatanta da 1.61mbpd da aka samu a kwata na daya da kuma 1.67mbpd da aka samu a daidai lokacin a shekarar 2020.

A gefe guda, bangaren da ba na mai ba ya karu da 5.44% a cikin kididdiga kwata-kwata (Q3 2021). Ci gaban da aka samu a fannin da ba na man fetur ba ya samo asali ne ta hanyar kasuwanci, watsa labarai da sadarwa (Telecommunication).

Sauran bangarorin sun hada da Kudi da Inshora (Cibiyoyin Kudi); Masana'antu (Abinci, Abin sha & Taba); Noma (Kayan amfanin gona); da Sufuri da Ajiya (Sufurin Hanya).

A zahiri, bangaren da ba na mai ya ba da gudummawar 92.51% ga GDP na kasar a cikin kwata na uku na 2021, mafi girma daga rabon da aka samu a kwata na uku na 2020 wanda ya kasance 91.27% kuma kasa da kwata na biyu na 2021 da aka samu wanda ya kai 92.58%.

Kara karanta wannan

Charles Soludo: Muhimman abubuwa 10 da ya dace ku sani game da zababben gwamnan Anambra

Tsadar rayuwa: Sayen kayan abinci a Kogi da Jigawa ya fi Legas tsada yayin da farashi ya karu a Oktoba

A wani labarin, Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin kayayyakin abinci a kasar ya sake tashi a watan Oktoban shekarar 2021, duk da faduwar farashin kayayyaki karo na 7 a jere zuwa kashi 15.99%.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na farashin kayan masarufi da ta buga a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin, 15 ga Nuwamba, 2021.

A hakikanin gaskiya, adadin hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba na 15.99% shine adadi mafi kankanta a cikin watanni 10 da suka gabata. Tun daga farkon shekarar 2021 (Janairu zuwa Oktoba), alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 17.28%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel